✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cikar NATO Shekara 70: Trump da Erdogan sun caccaki Macron na Faransa

A yayin taron Kungiyar Tsaro ta NATO da ya gudana a Birtaniya, Shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana furucin da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron…

A yayin taron Kungiyar Tsaro ta NATO da ya gudana a Birtaniya, Shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana furucin da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron ya yi cewar ‘Hadakar NATO ya susuce’ inda Trump ya ce kalaman cin fuska ce ga kungiyar.

Ya bayyana furucin a matsayin ‘mummunan kalami, wanda yake cike da nuna rashin mutunci ga NATO.’

Shugaba Macron ya yi wadannan kalamai ne a wata zantawa da mujallar The Economist ranar 7 ga watan jiya yayin da yake sukar lamirin NATO sakamakon rashin wani katabus da kungiyar ta yi game da farmakin da Turkiyya ta kaddamar a baya-bayan nan a kasar Syria. Sai dai daga bisani, Shugaban  Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya mayar wa Macron martani, inda ya kalubalanci Shugaban na Faransa da ya nazarci kwakwalwarsa kan ‘ita ce ta susuce.’

Shugabannin kasashen da ke cikin Kungiyar NATO za su yi kokarin dinke barakar da ke tsakaninsu, a taron da ya dada nuna rarrabuwar kawuna sakamakon rashin jituwa da kuma makomar kungiyar da ke cika shekara 70.

Irin wannan taro da aka yi na shugabannin a bara ya kare da rashin fahimtar juna, inda Shugaba Trump na Amurka ya bukaci takwarorinsa na Turai su rika biyan kudaden da aka gindaya musu abin da ya sa shi karo da shugaban Faransa Emmanuel Macron.

Shugaba Macron ya bukaci a sake tattaunawa da Rasha da kuma bukatar Turkiyya ta yi bayani kan dalilin da ya sa ta kai wa dakarun Kurdawan Syria hari da kuma sayen makamai daga Rasha.

A ranar Talata shugabannin sun gudanar da tarurruka daban- daban a tsakaninsu, kafin daga bisani suka ci abincin dare da Sarauniyar Ingila, Elizabeth ta Biyu a Fadar Buckingham, amma Shugaba Macron bai janye matsayinsa ba na cewa kungiyar ta kauce hanya, yayin da Shugaba Trump ke ci gaba da nanata matsayinsa na ganin kowace kasa ta biya kudin ka’idar da aka gindaya mata.

Shugabannin sun taru a otel Watford a Arewacin Landan na sa’oi uku, kafin bayyana matsayin da suka cimma, yayin da Firayi Ministan Birtaniya, Boris Johnson ya yi kiran inganta hadin kai a tsakaninsu.

Shugabannin kasashen duniya da dama ne suka hallara Landan, domin taron na wuni biyu na bikin cikar Kungiyar NATO shekara 70 da kafuwa.