An kwashe kimanin kwanaki uku a wannan mako ana gudanar da shagulgulan taya kungiyar kwadago ta kasa (NLC) murnar cika shekara 40 da kafuwa. An kafa kungiyar ce tun a shekarar 1978. Don haka muna yaba wa kungiyar wajen jajircewa da kuma kokarin kwatowa ma’aikatan kasar nan hakki. A ranar Juma’ar da ta gabata ce aka gudanar da addu’o’i a Masallatai daban-daban na kasar nan yayin da aka gudanar da irin wadannan addu’o’i a Coci-Coci da ke fadin kasar nan.
A shekarar 1978 ce aka kirkiro da kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da hakan ta dunkule ta zama daya da kungiyoyin kare hakkin ma’aiata hudu da ake da su kafin wannan lokaci. Kafin nan akwai kungiyar ’yan kasuwa mai suna Nigerian Trade Union Congress (NTUC), da ta Labour Union Front (LUF) da ta United Labour Congress (ULC) da kuma ta Nigerian Workers Council (NWC). An kirkiro da kungiyar NLC ce a karkashin wata doka a lokacin mulkin soja. A da akwai kungiyoyin kwadago kimanin dubu 1 da hakan ta sa aka markade su suka koma 42 kuma dukkansu sun kasance ne a karkashin babbar kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da suke magana da murya daya.
Sai dai kawo yanzu kungiyar NLC ta fuskanci kalubale masu yawa. Alal misali a shekarar 1988 a lokacin mulkin Shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida ya taba rushe kungiyar saboda adawar da ta nuna a shirinsa na tsuke bakin aljihu (Structural Adjustment Progamme, SAP) da kuma karin kudin fetur. Daga nan ne aka zabi Kantoman riko wanda ya ci gaba da gudanar da harkokin kungiyar a shekarar 1994. Sannan a zamanin mulkin Shugaban kasa Janar Sani Abacha ma ya taba rusa kungiyar NLC kuma ya maye gurbinta da Kantoman riko saboda yadda kungiyar ta nace wajen mayar da tsarin gwamnati ya koma irin na farar hula.
kungiyar kwadago ta yi shugabannin da suka shahara a Najeriya. Shugabanta na farko shi ne Cif Micheal Imoudu wanda aka haifa a shekarar 1902. Shi ne shugaban farko na kungiyar kwadago da a lokacin ake kira da kungiyar Ma’aikatan Jiragen kasa (Railway Workers Union, RWU). A lokacin shugabancinsa, ya yi kokarin wajen ganin an kara wa ma’aikata albashi, da mayar da ma’aikatan da aka dauka a matsayin na wucin-gadi zuwa na dindindin da kuma samar musu da ingantattun kayayyakin aiki.
Shugaban NLC na farko a shekarar 1978 shi ne Alhaji Hassan Summonu wanda Ali Ciroma ya maye gurbinsa a shekarar 1984. Yayin da marigayi Pascal Bafyau ya zama shugaban NLC a tsakanin shekarar 1988 zuwa 1994.
Amma shugaban NLC da ya fi shahara kawo yanzu shi ne Adams Oshiomhole wanda ya fito daga kungiyar kwadago reshen masaku a zaben da aka yi a shekarar 1999. A shekarar ce kasar nan ta koma kan turbar mulkin dimokuradiyya. Daga cikin nasarorin da ya samu sun hada da na jagorantar yajin aiki a kan karin farashin fetur sannan ya jagoranci ganin an yi wa ma’aikata karin albashi da kashi 25 cikin 100 a zamanin mulkin shugaban kasa Olusegun Obasanjo. Daga baya ya zama Gwamnan Jihar Edo. Bayan shi sai aka zabi Kwamared Abdulwaheed Omar a matsayin shugaban NLC a shekarar 2007. Daga nan ne aka zabi shugaban NLC na yanzu wanda ya fito daga kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya ta kasa (Health Workers Union), Kwamared Ayuba Wabba a shekarar 2015.
A shekarun baya, kungiyar NLC ta zame wa gwamnati ala kakai, inda da zarar ta furta aniyarta na shiga yajin aiki, za ka tarar gwamnati ta kidime. Amma a yanzu alamu sun nuna kungiyar ba ta da kima a idon gwamnati da ma’aikata da kuma sauran al’ummar kasa. kalubalen da kungiyar take fuskanta a halin yanzu sun hada da na rashin samun hadin kai a tsakanin shugabannin kungiyar, da yadda darajarsu ta zube a idon ma’aikata da sauran al’ummar kasa da kuma yadda aka samu tabarbarewar tattalin arzikin kasa da sauransu.
A zaben da kungiyar NLC ta gudanar wanda Kwamared Ayuba Wabba, shugaban kungiyar na yanzu ya samu nasara Kwamared Joe Ajaero Sakatare-Janar na kungiyar ma’aikatar wutar lantarki wanda suka yi takarar wannan kujera tare ya nuna bai amince da sakamakon zaben ba.. A bara ne Joe Ajaero tare da hadin gwiwar shugaban kungiyar masu dakon man fetur da iskar gas (NUPENG) suka bayar da sanarwar kafa sabuwar kungiyar kwadago mai suna United Labour Congress (ULC). Duk da gwamnati ba ta san da zaman wannan kungiya ba, amma hakan yana kawo wa NLC nakasu.
Abin takaici shi ne yadda NLC ta nemi a shiga yajin aiki a shekarar 2016 bayan gwamnati ta kara kudin mai daga farashin Naira 97 a kowace lita zuwa Naira 145 amma membobinta da al’ummar kasa suka yi biris suka ki shiga yajin aikin da hakan ya sa ta janye ba tare da ta cimma buri ba. Wannan ya nuna darajar kungiyar ya fara zubewa a idon al’umma.
A yanzu da kungiyar ta cika shekara 40 da kafuwa, muna kira da ta yi kokarin dinke barakar da ke tsakaninta don ta dawo da kimarta a idon duniya da hakan zai sa ta ci gaba da gwagwarmayar da take yi na kwato wa ma’aikata da ’yan kasa hakki.
Don haka Aminiya na taya kungiyar murnar cika shekara 40 da kafuwa da fatan za ta ci gaba da fafutukar kwatowa ma’aikata da talakawa hakki.