✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ci-Garin Katsina ya riga mu gidan gaskiya

Za a yi jana'izarsa ranar Alhamis a Katsina

Allah ya yi wa Ci-Garin Katsina, Alhaji Aminu Mamman Dee, rasuwa.

Ya rasu da yammacin Laraba bayan ’yar gargajeruwar rashin lafiya.

Ya rasu a Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Jihar Katsina.

Kafin rasuwarsa, Marigayi Aminu Mamman Dee babban amini ne ga Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman.

Za a yi jana’izar shi a ranar alhamis da misalin karfe 10:00 na safe a Fadar Sarkin na Katsina