Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea ta nada tsohon dan wasanta, Frank Lampard a matsayin mai horaswa na wucin gadi.
Karo na biyu ke nan da Lampard ya zama kocin Chelsea, bayan sallamar sa da kungiyar ta yi a 2021.
Ta nada Thomas Tuchel a matsayin wanda ya maye gurbinsa, amma kwalliya ta gaza biyan kudin sabulu a farkon kakar wasanni ta 2023.
Chelsea ta sallami Tuchel daga aiki ta kuma nada Graham Potter a matsayin sabon kocinta.
Shi ma Potter ta sallame shi a satin da ya wuce bayan gaza yin katabus a wasanni 32 da ya jagoranci kungiyar.
Lampard, ya kasance a zaune babu aiki tun a watan Janairu da kungiyar kwallon kafa ta Everton ta sallame shi daga aiki.
Wasanni tara ne suka rage wa Chelsea a gasar Firimiyar Ingila, inda take a matsayi na 11 a teburin gasar.
A sati mai zuwa kungiyar za ta barje gumi da Real Madrid a Gasar Zakarun Turai.