Chelsea ta zama zakara a gasar cin Kofin Zakarun Turai, UEFA Champions League, inda ta yi nasara a kan Manchester City a wasan karshe.
Chelsea ta zura kwallo daya tilo a wasan ta hannun dan wasanta, Kai Havertz, a minti na 42 kafin tafiya hutun rabin lokaci.
- Chelsea da City za su fatata a wasan karshe na Kofin Zakarun Turai
- An sake kone ofishin ’yan sanda a Imo
- Juyin mulki: Shugaban Mali da Fira Minista sun yi murabus
Nasarar da Chelsea ta samu a ranar Asabar ya sa ta lashe gasar karo na biyu a tarihinta.
Kocin Chelsea, Thomas Tuchel, ya kafa tarihi a kungiyar, wanda ya karbi ragamarta a watan Janairu, bayan Chelsea ta sallami Frank Lampard.
Kazalika, a karo na uku kenan da Chelsea ta doke Manchester City, ciki har da nasarar da ta yi a wasan daf da na karshe na gasar kofin kalubalen Ingila wato FA Cup.
Yanzu dai Chelsea ta zama jagaba kuma zakara a nahiyyar Turai, bayan ta yi nasara a kan Manchester City da ci daya mai ban haushi.
Sai dai fitaccen dan wasan tsakiyar Manchester City, Kevin De Bruyne, ya ji rauni a minti na 56, sakamakon karo da ya yi da dan wasan baya na Chelsea, Rudiger.
Samun rauni da De Bruyne ya yi, ya kawo Manchester City nakasun samun karsashi a wasan wanda hakan ya janyo mata cikas.