✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chelsea ta ki karbar tayin United kan Mason Mount

Chelsea na neman fam miliyan 70 gabanin rabuwa da Mason Mount.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi watsi da tayin fam miliyan 40 da Manchester United ta yi kan dan wasanta Mason Mount.

Erik ten Hag dai na fatan kawo Mount mai shekaru 24 Old Trafford don cike masa gibin da ya ke da shi a bangaren ‘yan wasan gaba masu zura kwallo.

Sai dai matashin dan wasan na Ingila na da sauran shekara guda a kwantiragin da ke tsakaninshi da Chelsea wanda ya san kungiyar ke neman fam miliyan 70 gabanin rabuwa da shi, farashin da United ke ganin ya yi matukar tsada kan dan wasan.

Wannan mataki na United game da farashin Mount shi ke fayyace cewa abu ne mai wuya kungiyar ta iya sayen Harry Kane na Tottenham da aka sanyawa farashin fam miliyan 100 duk kuwa da yadda ake jita-jitar ta fara tattaunawa da dan wasan.

Mount dai ya samu horo ne a kwalejin ’yan wasa masu tasowa ta Chelsea makaranta da ya faro tun yana shekaru 6 da haihuwa.

Ya shafe tsawon lokaci matsayin aro a kungiyoyin kwallon kafa na Derby County da Arnhem gabanin fara dokawa Chelsea wasa a shekarar 2019.

A cikin kakar wasa 3 da ya haska, ya taimaka wa kungiyar lashe Kofin Zakarun Turai ko da yake ya gamu da matsala a wannan kaka sakamakon doguwar jinya.