✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa na ba Gwamna Zulum kyautar kwandon mangwaro – Bazawara

Gwamnan ya karba yai mata godiya, sannan ya ba ta kudi

Wata bazawara kuma mahaifiyar yaya shida, ta mika kyautar kwando cike da mangwaro don karfafa gwiwar Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya ci gaba da ayyukan alheri a fadin jihar.

Aminiya ta rawaito cewa matar, mai suna Zulai Mohammed, wacce wani direban dan kasuwa ya bige mijinta kuma daga bisani ya mutu sakamakon raunin da ya samu, ta fara sayar da mangwaro da ’ya’yan itatuwa na kayan marmari domin kula da kanta da ’ya’yanta shida.

Matashiyar wacce ta fito daga garin Mallam Kyari, Karamar Hukumar Mafa ta Jiihar, ta yi matukar farin ciki da haduwa da Gwamnan,wanda ke ziyarar gani da ido kusa da unguwarsu da ke kan titin Maiduguri zuwa Mafa, kuma ba ta bata lokaci ba ta mika masa kwandon mangwaron nata.

Ta ba shi mangwaron ce a matsayin kyauta saboda jin dadin arbar da suka yi da shi.

A cewar ta, “Gwamna Zulum tamkar wani Bawan Allah ne da Allah ya aiko domin ya ’yantar da mutanen Borno daga rashin ci gaba da talauci da ya dabaibaye su sakamakon rikicin Boko haram da yankin ya yi fama da shi na tsawon lokaci.”

“Yau daya ce daga cikin mafi kyawun ranaku a rayuwata, na samu damar tattaunawa kai tsaye da Gwamna na, na yi farin ciki sosai, shi ya sa na ba shi kwandon mangwaro na kyauta don karfafa masa gwiwa ya ci gaba da ayyukan alheri na bunkasa Borno da kuma ‘yan kasa.”

Zulai ta bayyana cewa shekaru 12 da suka gabata ita da ’ya’yanta shida suna zaune a cikin wani kuntataccen gida tun bayan rasuwar mijinta.

Gwamna Zulum a lokacin da yake karbar mangwaron, ya mika wa Zulai wasu kudade, tare da bai wa wasu da suka yi wa ayarin motocinsa kawanya.

Tun da farko, Farfesa Zulum ya duba wasu ayyuka inda ya kara bayyana aniyarsa ta aiwatar sabbin ayyukan raya kasa a wa’adinsa na biyu.