✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun lalata masana’antar kera bama-bamai ta ISWAP a Borno

Sojojin sun kuma ce sun kashe 'yan ta'addan da dama

Rundunar sojin saman Najeriya ta kashe mayakan kungiyar ISWAP da dama tare da lalata wata masana’antarsu ta kera abubuwan fashewa a kusa da yankin Tafkin Chadi.

Hare-haren wadanda Manjo Janar Ibrahim Ali, kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai da ke Arewa maso Gabas ne ya jagoranta.

An kuma yi amfani da jiragen yaki wajen kai harin a ranar Laraba a Tumbun Bakkassi, daya daga cikin wuraren da aka gano ’ya ta’addan na amfani da su wajen kera bama-bamai.  .

Wata majiyar leken asiri ta shaida wa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi cewa hukumar leken asiri ta bankado cewa ISWAP ta shirya tare da ajiye ababen fashewa tare da bayyana aniyar tura su a wurin sojoji dake Arege a Karamar Hukumar Abadam.

Wata majiyar sojan ta bayyana cewa harin na daga cikin hare-haren ramuwar gayya da tsojojin suka kai ta sama kan ’yan ta’addan bayan yunkurinsu na kai hari a sansanin sojojin Najeriya da ke Mallam Fatori.

Kazalika, bayanai sun nuna cewa wani jirgin saman sojojin da ke karkashin rundunar sojojin sama na Operation Hadin Kai ya kai wasu hare-hare ta sama a kan wuraren da ’yan ta’addan ke da sansani a Tumbun Shittu da ke kusa da Tafkin Chadi wanda aka tabbatar da samun nasara sosai yayin da aka kuma halaka ’yan ta’adda da dama.

Tun daga ranar 6 ga watan Yunin 2023, rundunar sojojin saman Najeriya ta fara kai hare-hare ta sama a yankin Arewa maso Gabas a karkashin shirin da ake yi wa lakabi da: OPERATION WARUN 3, wanda ya yi sanadin kawar da ’yan ta’addan Boko Haram fiye da dari, kwamandojin runduna da manyan mayaka a tsaunin Mandara a Karamar Hukumar Gwoza.