Rahotanni daga Ndjamenan kasar Chadi na cewar, gwamnatin mulkin soji kasar ta umurci jakadan kasar Jamus, Jan Christian Gordon Kricher, da ya bar kasar na nan da kwanaki biyu.
A wata sanarwa da suka fitar ta bakin kakakin gwamnatin kasar, hukumomin na Chadi sun ce sun yake shawarar korar jakadan na Jamus ne saboda ba ya mutunta dokokin diflomasiyya sannan mutum ne da ke yin katsalanda ga harkokin cikin gida na kasar.
- Yadda za a kawo karshen rikicin Rasha da Ukraine —Xi Jinping
- An kashe mahaifin dan kasuwa an sace shi a Birnin Tarayya
DW ya rawaito cewa, ya zuwa yanzu jakadan bai kai ga mayar da martani kan wannan batu, inda ba wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Kasar ya fidda kana ba wata sanarwa da aka samu daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Jamus din.
Gabanin wannan sallama da aka yi wa jakadan dai, ya sha sukar hukumomin kasar kan jinkirta gudanar da zaben Shugaban Kasa da kokarin da ake yi na share wa shugaban da ke rikon kwarya, Mahmad Idriss Deby, hanya ta nema shugabancin kasar.