Babban Bankin Najeriya CBN ya sanar da sake karya farashin Dalar Amurka a wani yunƙurin na sauye-sauye da yake yi domin farfaɗo da darajar Naira.
Babban bankin ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafinsa na intanet ranar Litinin.
Babban bankin ya ce a yanzu ya shirya sayar da Dala 10,000 ga kowanne kamfanin canji a kan N1101.
CBN ya kuma umarci ’yan canjin da su sayar da dalar kan ƙarin ribar da ba ta wuce kashi 1.5 cikin 100 kan farashin nasa ba.
Faɗuwar da darajar nairar ta dinga yi a makonnin da suka wuce ta jawo ɗaukar matakai daban-daban daga ɓangaren hukumomi ciki har da kama ’yan kasuwar canjin da jami’an tsaro suka yi a manyan birane kamar Kano, da Abuja, da Legas.
Aminiya ta ruwaito cewa, a makonnin bayan nan ne kasuwar bayan fage ta ’yan canjin kuɗaɗen ƙetare a Najeriya, darajar Naira ta ci gaba da ƙaruwa a yayin da farashin Dalar Amurka ke sauka.
Wani binciken da shafin Nairametrics ya gudanar, ya bayyana cewa farashin Dalar na ci gaba da sulalowa ne sakamakon yadda mutanen da a baya suka ɓoye Dalar amma a yanzu suka fito da ita domin sayarwa sakamakon rashin daraja da dalar ke fuskanta.
A yayin zantawar jaridar da wani dan kasuwa mai suna Musa, ya bayyana cewa sun yi farin ciki da yadda farashin Dalar ke kara karyewa.
Musa ya bayyana cewa wannan zai ba su damar gudanar da kasuwancinsu cikin kwanciyar hankali.