Babban Bankin Najeriya CBN, ya bayar da umarnin haramta sayar da Dala ga ’yan kasuwar canji nan take.
Gwamnan Bankin, Godwin Emiefele ne ya sanar da hakan ga manema labarai bayan wani taron Kwamitin Tsare-Tsaren Kudi na Kasa (MPC) da Bankin ya gudanar.
A cewarsa ba wa ’yan canjin kadai kudaden da yawansu ya kai Naira biliyan 5.7 a duk mako ba abu ne mai dorewa ba.
Ya bayyana cewa a halin yanzu a duk mako CBN na ba wa ’yan canji Dala miliyan 110, inda kowanne daga cikin kamfanonin canji sama da guda 5,500 da ake da su a Najeriya ke samun Dala 20,000 duk mako.
Kazalika, ya ce Babban Bankin ya rufe yi wa sabbin ’yan canji rajista, kuma yanzu duk wata hada-hadarsu za ta koma hannun bankunan kasuwanci da ke fadin kasar.
Aminiya ta ruwaito cewa, a yanzu duk bankunan kasuwanci za su tanadi sashen hada-hadar kudaden ketare a dukkan rassansu da ke fadin kasar.