Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bukaci ɗaukacin ’yan canjin kuɗaɗen ƙasashen ƙetare su sake rajista domin ci gaba da harkokinsu.
Babban bankin ya bayar da wannan umarni ne a wata takarda da Daraktan Sashen tsare-tsaren harkokin kudi na bankin, Haruna Mustafa ya fitar a ranar Laraba.
“Ana umartar ’yan canjin su cika sharuddan babban bankin na mallakar lasisin u cikin watanni shida.
“Sannan, duk ’yan canjin su sani cewa suna da damar neman kowane irin lasisi kamar yadda doka ta tanadar,” in ji sanarwar.
- NAJERIYA A YAU: Shin Ganawar Atiku Da Obi Na Kaɗa Hantar APC?
- Kotu ta bai wa Abba Kyari damar halartar ta’aziyyar mahaifiyarsa
Bankin ya kuma yi wasu sauye-sauye a tsarin gudanar da hada-hadar canji.
Daya daga ciki shi ne soke biyan kudin kafin alkalami na tilas har na Naira miliyan 200 ga masu lasisin mai daraja ta daya.
Haka kuma, bankin kolin ya kuma soke biyan kudin kafin alkalami na dole na Naira miliyan 50 ga masu rike da lasisin mai daraja ta biyu.
Bankin na CBN ya kuma soke kudin sabunta lasisi na shekara-shekara.