✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa za ta binciki korar ma’aikata 600 a CBN

Bai kamata a riƙa asarar ma’aikatan da aka bai wa horo kan ƙwarewar aikin banki ba.

Majalisar Wakilai ta bayyana damuwarta kan yadda hukumar Babban Bankin Nijeriya CBN ta sallami ma’aikata har guda 600.

A zamanta na ranar Laraba, majalisar ta umarci kwamitocinta masu kula da harkokin bankuna da su binciki yadda babban bankin kasar ya  sallami ma’aikata har guda 600, da ake zargin an yi ba bisa ka’ida ba.

Kudurin ya biyo bayan wata buƙata ta gaggawa da dan majalisar Jonathan Gaza Gbefwi  daga Jihar Nasarawa ya gabatar.

Dan majalisar ya soki korar ma’aikatan da ya ce an yi ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa wannan mataki zai dakushe kwarjinin bankin, kuma zai karya gwiwar ma’aikatan.

Ya ce, bai kamata a riƙa asarar ma’aikatan da aka horar da su, suka kware a fannoni da dama na aikin banki ba.

Majalisar ta amince da kudurin, ta kuma bukaci kwamitocin kula da harkokin bankuna su yi bincike, kuma su ba ta rahoto kan lamarin cikin makonni hudu.