✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ƙwace Kuɗaɗe da kadarori na Emefiele

Mai shari’a Bogoro ya bayyana cewa, duk waɗannan kadarori da kuɗaɗe ne na wasu ayyuka da suka saɓawa ƙa’ida,

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta bayar da umarnin a ƙwace Dala miliyan 4.7 da Naira miliyan 830 da wasu kadarori da dama da ke da alaƙa da tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele.

Da yake yanke hukunci a ranar Juma’a, Mai shari’a Yellim Bogoro, wanda a baya ya yi watsi da buƙatar kama Emefiele, ya amince da buƙatar hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC, wadda lauya Bilkisu Buhari-Bala ta wakilta.

Kuɗaɗen da a halin yanzu gwamnatin tarayya ta ƙwace, sun kasance a cikin asusun bankunan: First Bank, Titan Bank da Zenith Bank da wasu mutane da hukumomi suke kula da su da suka haɗa da: Omoile Anita Joy, kamfanin Deep Blue Energy Serɓice Limited, kamfanin Exactquote Bureau De Change Ltd, Kamfanin Lipam Investment Services Limited, kamfanin Tatler Services Limited, kamfanin Rosajul Global Resources Ltd, da kamfanin TIL Communication Nigeria Ltd.

Mafi yawan kadarorin da kotun ta miƙa wa Hukumar EFCC suna a jihar ta Legas ne, waɗanda suka haɗa da:

  • Gini mai hawa 11 – Ikoyi, Legas
  • AM Plaza, mai hawa 11, Lekki Peninsula 1, Legas
  • Imore Industrial Park, Ƙaramar hukumar Amuwo Odofin, Legas
  • Mitrewood and Tatler Warehouse, Ibeju-Lekki, Legas
  • Gine-gine buda biyu da ke Lakes Estate, Lekki, Lega

Mai shari’a Bogoro ya bayyana cewa, duk waɗannan kadarori da kuɗaɗe ne na wasu ayyuka da suka saɓawa ƙa’ida, waɗanda gwamnatin tarayyar Najeriya za ta iya kwace  su.

Alƙalin ya ce: “Na ga cewa ayyukan waɗanda ake ƙara a nan ba halastattu be ne. Me zai sa su samu matsalar dala nan take, Godwin Emefiele ya bar CBN a matsayin gwamnan Banki kuma an kasa biyan albashi?