Dan wasan gaba na Manchester United, Edinson Roberto Cavani Gómez, ya tsawaita yarjejeniyar zamansa a kungiyar har zuwa watan Yunin shekarar 2022.
A Litinin din da ta gabata ce dan wasan na Kasar Uruguay, ya rattaba hannu kan tsawaita wa’adain kwantaraginsa da kungiyar da karin shekara guda.
- An kama masu kwacen waya a Sallar Tahajjud a Kano
- Kayan Sallah: Dandalin sada zumunta ya tallafa wa marayu 100 a Kano
Cavani mai shekara 34 a duniya, na daya daga cikin fitattun ’yan wasan United da suka taka rawar gani a wasannin da ta fatata a ciki da wajen Ingila tun farkon kakar bana kawo yanzu.
A makonnin bayan nan ne dan wasan ya jefa kwallaye takwas, tare da ba da gudunmuwar cin wasu kwallaye uku cikin wasanni bakwai da ya haska.
A watan Oktoban 2020 ne Cavani ya zo United kyauta yayin da ake cin kasuwar musayar ’yan kwallo, inda a kakar bana ya jefa kwallaye 15 cikin dukkanin wasannin da ya buga kuma 9 daga cikin kwallaye ya jefa su ne a gasar Firimiyar Ingila.
Cavani na daya daga cikin ’yan wasan da suka bayar da gudunmuwa yayin da United ta lallasa Aston Villa 2-1 yayin haduwarsu ranar Lahadi a gasar Firimiyar Ingila.
Dan wasan ya kasance daya daga cikin manyan ’yan wasan gaba a fagen kwallon kafar Turai da tauraruwarsu ta haska a shekaru goman da suka gabata, inda ya ci kwallay 200 a wasanni 301 da ya buga wa PSG bayan zuwansa daga Napoli, kungiyar da ya yi suna.
Cavani ya bar PSG ta Faransa a watan Yunin 2020 bayan samun sabani da dan wasan gaba na Brazil, Neymar Jr.
A yanzu haka dai Kocin United, Ole Gunner Solskjaer, ya ce burinsa na ganin Cavani tya ci gaba da zama a kungiyar har zuwa kakar wasannin badi ya gama cika.