✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Canjin kudi ya goge duk alheran mulkin Buhari – Soyinka

Ya ce Shugaban ya bata rawarsa da tsalle a karshen mulkinsa

Fitaccen marubucin nan na Najeriya, Farfesa Wole Soyinka, ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bata rawarsa da tsalle saboda kirkiro sauya fasalin kudi yana dab da barin mulki.

Soyinka ya ce matakin ya goge dukkan alheran Shugaban kuma zai bar mulki a daidai lokacin da ’yan kasar ke fushi da shi.

Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Arise ranar Laraba, inda ya ce matakin ya jefa ’yan kasa cikin tsaka mai wuya.

Sai dai ya yaba wa wasu Gwamnonin Jihohi da suka yi ta maza suka kalubalanci matakin a kotu, inda ya bayyana hakan a matsayin Dimokuradiyya ta zahiri.

Ya ce, “Ni a ganina, bai ma kamata mu bata wani lokacinmu mai amfani ba wajen auna gwamnatin Buhari, saboda zai tafi kowa na jin haushinsa.

“Ina magana ne a kan abin da dare daya ya jefa miliyoyin ’yan Najeriya cikin halin ni-’ya-su. Ina fargabar da za a fita jin ta bakin jama’a, to da za a fahimci cewa wannan matakin guda daya ya goge dukkan alheran gwamnatinsa.” in ji Soyinka.

Kazalika, marubucin ya gargadin ’yan Najeriya a kan yada labaran karya, inda ya karyata wani labari da ake yadawa a kansa a kafafen sada zumunta na zamani.

Ya kuma yi alkawarin bayar da tukwicin Dalar Amurka 1,000 ga duk wanda ya taimaka wajen zakulo wadanda suka kirkiri labarin tun da farko, wanda ake alakantawa da shi.