✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Canjin kudi: Talakawa kawai ake wahalarwa —Kwankwaso

Wadanda aka yi canjin kudin domin su, ko a jikinsu

Dan takarar shugabancin kasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya zargi Babban Bankin Najeriya (CBN) da gana wa talakawa azaba da sunan sauya fasalin Naira.

Ya ce wahalar da sauyin ya haifar ba zai shafi attajiran kasar ba saboda su ke da bankuna.

“Kamata ya yi gwamnati ta zama mai magance matsalolin jama’a, ba jefa su cikin ukuba ba,” in ji shi.

Kwankwaso ya ya yi wannan bayani ne a wani shirin gidan Talabijin din Channels ranar Alhamis.

Ya ce jiga-jigan ’yan siyasa musamman ’yan takarar shugabancin kasa, ko nawa suke bukata za su samu, saboda alakarsu da bankuna.

“Mu a NNPP ba mu gamsu da wa’adin wata uku da ma karin kwana 10 da ake magana ba.

“Da yawan mazauna Abuja, wadanda ke zaune hankalincinsu kwance a gida ko ofis, ba za su fahimci abin da ke wakana a waje ba.

“Gwamnati ta yi abin da ta yi ne saboda wadanda za su ciri makudan kudi, kamar shugabanni da ’yan siyasa.

“Ba su san cewa da yawan ’yan uwanmu ’yan takara, musamman na shugaban kasa da mamabobin jam’iyyarsu su ne ke da bankuna ba.

“Haka ma makusantansu na da bankuna a ko’ina, don haka babu wata asarar da za su yi.

“PDP na da gwamnoni haka ma APC, kawo yanzu gwamnoni sun karbi makudan kudade daga bankunan da ke jihohinsu,” in ji Kwankwaso.

An ambato Shugaba Buhari ya ce an dauki matakin canja kudin ne don yi wa ’yan rashawa illa.

Haka nan, ya ce gwamnati ba za ta bari talakawan Najeriya su fusknaci wani matsi saboda daukar matakin ba.

Sai ga shi an wayi gari samun tsaffin takardun Naira sun gagari talaka balle kuma sabbin, lamarin da ya jefa ’yan kasa cikin mawuyacin hali.

%d bloggers like this: