✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Canjin Kudi: Buhari ya yi gum bayan cikar wa’adin da ya bayar

Shugaba Buhari ya ki ce wa ’yan Najeriya uffan bayan cikar kwana bakwai da ya ce a ba shi zai yanke shawara kan makomar dokar…

Shugaba Buhari ya ki ce wa ’yan Najeriya uffan bayan cikar kwana bakwai da ya ce a ba shi zai yanke shawara kan makomar dokar hana amfani da tsoffin takardun kudi.

Ranar Juma’a ce karshen kwanaki bakwan da ya bayar, bayan wasu gwamnonin Jam’iyyrsa ta APC sun bukaci karin wa’adin daina amfani da tsoffin takardun N1,000, N500 da N200 da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sauya wa fasali.

A lokacin da ya bukaci kwana bakwai domin yin tunanin, Buhari ya ce, “Ko shekara daya aka kara ba za a rasa matsala ba,” tare da cewa CBN ya ba shi tabbacin cewa yana da karfin samar da wadatattun sabbin takardun kudin.

A ranar Juma’a da kwana bakwai din suka cika ne kuma shugaban kasar ya jagoranci taron Majalisar Koli ta Kasa, wadda ta kunshi tsoffin shugabannin kasa da kuma gwamnoni masu ci, inda aka tattauna matsalolin Najeriya, ciki har da batun sauyin kudin.

A karshen taron Majalisar Kolin, wadda ta karbi bakuncin Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ta umarci CBN ya samar da isassun takardun kudin da aka sauya, in ba haka ba a ci gada da amfani da tsoffin, har zuwa lokacin da sabbin za su wadata.

An yi zaman ne ’yan kwanaki bayan wasu gwamnonin APC (Nasir El-Rufai na Kaduna, Yahaya Bello na Kogi da Muhammad Bello Matawalle na Zamfara) sun maka Gwamnatin Tarayya da CBN a Kotun Koli suna neman ta hana aiwatar da dokar hana amfani da tsoffin takardun kudin.

Sai dai kuma bayan kammala taron har zuwa wannan lokaci shugaban kaa bai ce wa ’yan Najeriya komai kan lamarin ba.

Lamarin dai ya sa wasu ’yan Najeriya cikin rudani, musamman masu son jin bayani kan inda aka kwana daga Fadar Shugaban Kasa da kuma daga CBN kan yadda zai aiwatar da umarnin Kotun Koli da kuma na Majalisar Kolin wajen samar da isassun takardun kudi.

Kotun Koli dai ta hana aiwatar da dokar haramta tsoffin takardun kudin zuwa 17 ga watan Fabrairu da muke ciki, ranar da za ta saurari karar da gwamnonin suka shigar gabanta.

Ko da yake Gwamnatin Tarayya ta hannun Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ta shigar da bukatar neman Kotun Kolin ta yi watsi da karar gwamnonin.

Sai dai a wata hira da Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna ya yi da Malami, ya ce gwamnati za ta bi umarnin Kotun.

Ministan ya bayyana cewa duk da matsalolin da suka biyo bayan sauya kudaden, cikin ’yan kwanaki an fara ganin ribar sabuwar dokar ta CBN, ta fuskar raguwar ayyukan garkuwa da mutane da kuma karbar rashawa.

A nasa bangaren, CBN ya karyata rade-radin da ke yawo cewa gwamnan bankin ya shaida wa taron Majalisar Kolin cewa Kamfanin Buga Muhimman Takardu na Najeriya (NSPMC) ba shi da karfin buga kudaden.

Da yake karyata labarin, Daraktan Yada Labaran CBN, Osita Nwanisobi, ya bayyana cewa kamfanin NSPMC na da duk abin da ake bukata na buga takardun kudin da Najeriya ke bukata.

Ya kara da cewa, “Mista Emefiele ya shaida wa taron cewa yanzu haka NSPMC na aikin buga duk kudaden da ’yan Najeriya ke bukata domin gudanar da harkokinsu.”

Wannan ne karon farko a tarihi da Najeriya ta buga kudadenta a cikin gida.

Hakan ne ya sa Najeriya cikin jerin kasashen Afirka biyar da ke buga kudadensu a cikin gida.

Canjin kudin dai ya zo da matsaloli, musamman na rashin samun sabbin kudaden, wanda ya jefa akasarinsu da harkokin kasuwanci cikin damuwa.

Matsalar ta haifar da dogayen layikan cirar kudi a ATM da bakuna, inda a wasu wuraren aka samu barkewar rikici, har da tarzoma.

CBN dai ya zargi bankunan kasuwanci da boye sabbin takardun kudin da ya ba su, zargin suka musanta.