✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CAF ta daga wa Kano Pillars kafa

Hukumar shirya wasan kwallon kafa a Afirka (CAF) ta daga wasan da Kano Pillars za ta yi da kulob din Moghreb Tetouane na kasar Maroko…

Hukumar shirya wasan kwallon kafa a Afirka (CAF) ta daga wasan da Kano Pillars za ta yi da kulob din Moghreb Tetouane na kasar Maroko da mako daya a gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Afirka saboda abin takaicin da ya sameta a makon jiya, bayan ’yan fashi da makami sun tare su a Abuja a hanyarsu ta zuwa Owerri don buga wasan rukuni-rukuni na kasa da kulob din Heartland.

Biyar daga cikin ’yan kwallon ne suka samu rauni da hakan ta sa kulob din bai halarci gasar ba.
Wannan dalili ne ta sa ita ma Hukumar CAF a nata bangaren ta ce ta sauya ranar da kulob din zai yi wasa da na Maroko don ba kulob din da ’yan kwallonsa damar farfadowa daga harin ’yan fashin.
Hukumar ta ce wasan da Pillars za ta yi a ranar 14 ga wannan wata na Maris yanzu ya koma a tsakanin ranakun 20 zuwa 22 ga watan nan da muke ciki.
A wata sanarwa da kulob din na Pillars ya yi a kafar sadarwar twitter a ranar Litinin da ta wuce, kulob din ya tabbatar da samun kwafen wasika daga Hukumar CAF na amincewa da daga wasan.
“CAF ta daga wasanmu daga ranar 14 ga wannan wata zuwa ranakun 20 zuwa 22 ga wata saboda abin bakin cikin da ya same mu”, inji sanarwar.
Daga cikin ’yan kwallon da suka samu rauni a lokacin harin sun hada da Gambo Mohammed da Eneji Otekpa da Reuben Ogbonaya da Moses Ekpai da kuma Murtala Adamu.