Burkina Faso ta bude kofa ga kasashen da ke kawance da ita da su taimaka mata da dakarun soji don kawo karshen karshen tashe-tashen hankulan da ke sabbaba asarar rayukan dimbin fararen hula.
Firaminista Albert Ouédraogo, wanda gwamnatin mulkin sojan kasar ta nada tun bayan juyin mulki a karshen watan Janairu, ya sanar da matakin yayin gabatar da manufofinsu ga majalisar dokokin rikon kwarayar kasar a ranar Litinin.
Ouedraogo, ya bayyana cewar zabinsu a yanzu shi ne karkatawa don inganta dangartakar kawancen soji da wasu kasashe domin inganta hadin gwiwa da kuma tsaro, ta hanyar mutunta Burkina Faso a matsayin kasa mai cikekken ‘yanci.
Shugaban gwamnatin bai ambaci wata kasa su ke shirin kulla sabon kawancen sojin ba, yayin jawabin da ke zuwa dai-dai lokacin da Faransa babbar abokiyar kawancenta ta tarihi, ke janye sojojinta daga Mali.
Hakan na zuwa kwanaki kadan, bayan da shugaban rikon kwaryar kasar da ya jagoranci juyin mulki, Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba, ya sanar da kafa wani kwanitin cikin gida don tattaunawa da kungiyoyin masu dauke da makamai.