Shugaban kungiyar yaki da aikata ayyukan assha da dawo da matasa kan daidaitaccen tafarki da ke Jihar Ogun, Dokta Babatunde Olokun ya ce daga cikin manufofin kafa kungiyar akwai batun taimaka wa gwamnati domin samar wa matasa aikin yi tare da shuka musu halin da’a.
Dokta Babatunde yana magana ne sa’ilin da yake wa taron manema labarai jawabi a Abeokuta, fadar gwamnatin jihar ta Ogun, kuma ya bayyana cewa suna yekuwa a wurare daban-daban da suka san matattarar jama’a ce, kamar a kasuwanni da tasoshin mota, inda matasa suke harkokinsu na yau da kullum.
Ya ce suna yi wa matasan lacca ne tare da koya musu sana’o’i iri daban-daban ba tare da sun biya ko sisi. “Kodayake ba mu da tallafin da za mu ba su a matsayin abin da za su habaka sana’ar da suke da ita, yanzu haka muna tattaunawa da gwamnati kan yadda za ta sama musu tallafi a wannan fannin”. Inji shi.
Ya ce kungiyar ba ta da nasaba da siyasa, lamarin da suke fada wa matasan da kar su sake a rika amfani da su a matsayin ’yan bangan siyasa, abin da ke ingiza su suna shaye-shaye, wanda kuma hakan ke kara tura su aikata ayyukan assha.
Ya ce ba wanda ke biyan su ko sisi, yawancinsu kwararru ne a fannin ayyukansu kuma kowa a fannin da ya kware ne yake ba da gudunmowarsa, kuma yanzu haka sun samar wa sama da matasa 200 aikin yi a cikin garin Abeokuta kurum.
Ya ce mataki na gaba shi ne yadda za su fadada kungiyar zuwa sassan jihar, bayan ta kara samun ’ya’ya, domin wadanda suka koya kuma suka fara sana’ar, sun fara koyar da wasu, wanda hakan yana daya daga cikin yarjejeniyoyin da ake cimmawa tsakaninsu.
Shi ma Alhaji Salisu Ba-shan-kai, daya daga cikin shugabannin kungiyar, dan arewacin Najeriya, mazaunin garin Shagamu ya ce kofar kungiyar a bude take ga duk wanda yake zaune a jihar ta Ogun ba wai sai lallai Bayarabe ba.
Ya ce tuni ’yan Arewa da ke da sana’ar hannu suka shiga kungiyar kuma yaransu da ke garin Abeokuta suna cikin sahun wadanda suka amfana da kungiyar, kuma nan ba da jimawa ba kungiyar za ta fara harkokinta a garin Shagamu, kuma yana fata, ba Shagamun kadai ba, ta bazu har zuwa Arewacin Najeriya.
Burinmu shuka halin da’a ga matasan Najeriya -kungiyar Ceto Matasa
Shugaban kungiyar yaki da aikata ayyukan assha da dawo da matasa kan daidaitaccen tafarki da ke Jihar Ogun, Dokta Babatunde Olokun ya ce daga cikin …