✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in zama mai koyar da ilimi da tarbiyya – Binta Rabi’u Spikin

Tarihin rayuwarta:   Sunana  Hajiya Binta Rabi’u Spikin, kamar yadda na sha fada, shi Rabi’u Spikin Kakana ne, wanda ya haifi mahaifiya ta.   Ni Binta an…

Tarihin rayuwarta:  

Sunana  Hajiya Binta Rabi’u Spikin, kamar yadda na sha fada, shi Rabi’u Spikin Kakana ne, wanda ya haifi mahaifiya ta.   Ni Binta an haife ni ne a shekarar 1974 a Unguwar  Chediyar Kuda a Karamar Hukumar Birnin Kano.   A wancan lokacin duk dangina, mata ba a sa su karatun boko ba don haka sai Kakana, Alhaji Rabi’u Spikin, ya saka ni a makaranta, hakan ce ta sa nake amfani da sunansa har yanzu. Na yi firamaren da take gidan Kakan nawa, Mahmud Islamiyya Primary School, na yi sakandare daban-daban har 3.  Na fara daga Sakandare  ta Kabo, sai aka yi mini canjin makaranta zuwa Kwalejin ’yan mata ta Women Teachers Collages (WTC) Kano, sannan bayan na ci jarrabawar Kimiyya ta Science sai na tafi Sakandaren Kimiyya ta ‘Yan Mata (Girls’ Science Secondary School) Taura. Sannan na yi Difloma a bangaren  mulki da huldar jama’a wato Public Administration a Kwalejin koyar da sha’anin mulki ta School of Management Studies, daga nan na yi Digiri dina na farko a bangaren aikin jarida, a Jami’ar Bayero (BUK) ta Kano a shekarar 2011. A yanzu haka ni daliba ce a wannan jami’ar inda nake yin karatun Digiri na biyu wato Masters Degree a wannan fanni na aikin jarida. Na kuma halarci tarukan horarwa da na karin ilimi duk a wannan sashi na aikin jarida da na Kwamfuta a Ofishin Jakadancin Amurka da ke Najeriya a kan rubuta wasan Kwaikwayo an kuma ba ni takardar shaida wato Satifiket.

Aiki:

Na yi aikace- aikace da dama amma sai dai ba na gwamnati ba ne mafi yawansu, wato abin da ake kira Regular 9-5 Jobs,  yawanci na fi yin Consultancies wato aikin da zan yi a bangaren da nafi kwarewa a biya ni sai dai na taba yin aiki da Kamfanin Jaridar Triumph Publishing Company na Kano a matsayin ‘yar jarida inda daga baya na zama Mataimakiyar Editan Labarai na Musamman wato Assistant Features Editor, kuma ina yin irin wannan aiki a matsayin ‘yar jarida mai zaman kanta ma’ana Freelancer da BBC Media Action inda muke rubuta musu wasan Kwaikwayon nan na GA TA NAN GA TA NAN KU.

Nasara:

Na samu nasarori da yawa a aikace- aikacen da na yi  mafi girma a cikin su shi ne samun karbuwa a wurin mutane musamman matasa a Jihar Kano saboda yadda nake da su yanzu a Kano idan ka ce Binta Spikin sai ka ce Maman Matasan Kwankwasiyya wanda jama’a sun yaba irin aikin da na yi da kuma yadda nake mu’amulla da jama’a wannan kadai ba karamar nasara ba ce musamman ga ’ya mace a rayuwa.

Kalubale:

Kalubalen su ma akwai su musamman kasancewa ta mace mai gwagwarmaya a cikin maza.   Wasu mazajen ba a son ransu suke son ganin wata mace ta ci gaba ba amma cikin ikon Allah da aka fafata  sai na yi fice na zama zakara a cikin dubban mazaje.

Yawan iyali:

Alhamdulillahi ina da aure da kuma ‘ya’ya.

Kungiyoyi da kasashe:

Ina cikin kungiyoyi da yawa