Surajo Isma’ila saurayi dan shekara 23, dan asalin garin Rubochi ne da ke yankin Kuje a Babban Birnin Tarayya, Abuja. Ya halarci Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere da ke Garki, Abuja inda ya kammala a shekarar 2016.
A tattaunawarsa da Aminiya, Surajo, wanda ya sha wakiltar kwalejin da ya kammala a nukukuwa da dama inda ya ciyo mata lambobin yabo a matakai daban-daban, ciki har da wanda ya ci nasarar samu a kasar Brazil a shekarar 2011, ya ce ya fara hada tarakta ce da manyan motocin daukar kaya ta hanyar amfani da katan-katan din kwali tun yana makarantar firamare.
Surajo, ya ce sha’awar da ya taso da ita ta son harhada injuna daban-daban ta zamo sanadiyyar yin fice ciki har da halartar taron baje koli na Kasuwar Duniya da aka kammala a Abuja.
Ya ce burinsa tun yana karami shi ne ya zama injiniya sai dai rashin kula daga bangaren gwamnati da na masu zaman kansu wajen samun tallafi don fadada iliminsa a fagen da yake ganin yana da kwarewa shi ne babban kalubalen da yake fuskanta a halin yanzu.
“Duk da halartar Bikin Baje Koli na Duniya da na yi a Abuja inda na baje kolin irin fasahar da nake da ita a hanyar nuna wa duniya taraktocin da na kera ko sisin kwabo ban samu a matsayin wani tallafi daga bangaren gwamnati ko na kungiyoyi masu zaman kansu ba,” inji shi.
Ya ce idan har zai samu cikakken tallafi don ba shi damar mallakar kayayyakin hade-hade na zamani zai yi matukar amfanar da kasar nan ta hanyar bayar da gudunmawa a fannin tattalin arzikin Najeriya ta fuskoki da dama.
Ya ce ya dauki tsawon shekara biyu wajen hada tarakta kirar gida wanda ya nuna a wajen Bikin Baje Kolin Duniya da aka gudanar a Abuja.
Ya ce a tsawon lokacin da ya dauka yana kere-keren yana amfani ne da kwanon alminiyon inda kuma yake samun kudi ta hanyar ’yan kyaututtukan da ba su wuce Naira 50 zuwa 100 ba daga wadanda abin yake burge su idan ya fita yawon nuna wa jama’a irin baiwar da yake da ita. Ya ce babban damuwarsa ita ce samun tallafi daga gwamnati ko kungiyoyi, domin ’yar gudunmawar da yake samu daga wasu kungiyoyin ba za ta iya mallaka masa irin kayayyakin aiki na zamani da yake bukata ba don samun tsayawa da kafafunsa.
Ya ce a halin yanzu yana amfani ne da taraktar da ya kera wajen dibar ruwa yana saidawa a jarkoki a kullum inda yake samun kudin da yake amfani da su wajen sayen wasu kayayyakin yin walda da zai sake kera wata na’ura mai tafiya. Ya ce: “Babban burina yanzu shi ne kirkiro na’urar robot da za ta rika daukar jakunkunan matafiya a filin jirgin sama zuwa inda fasinjoji ke zaman jiran lokaci. A yanzu haka ina kan shirye-shiryen hada wannan mutum-mutumi da zai rika daukar kayan fasinjoji a filin jirgin sama.”
A karshe ya yi fatar samun tallafin sukolashif don karo ilimi a kasashen ketare, inda ya yi fatar ganin mafarkinsa ya tabbata.