Ya zuwa yanzu dai shaharar Dokta Bukar Usman a fagen rubuta littattafan ilimi ba voyayya ba ce. Ya yi fice wajen rubuta littattafan Ingilishi da na Hausa a fagagen al’amuran yau da kullum, aikin gwamnati da kuma Adabi. Xaya daga cikin mashahuran littattafansa a fagen Adabin Hausa, shi ne babban kundin littafin tatsuniyoyi mai taken Taskar Tatsuniyoyi. A kwanan nan ne kuma ya fitar da sabon littafin tarihin mahaifarsa, mai taken Tarihin Qasar Biu; wanda ya shafe tsawon shekaru tara yana aikinsa. Littafin ya samu yabo a ciki da wajen Najeriya, musamman daga hamshaqan malaman ilimi na jami’o’i daban-daban na wannan qasa. A wannan tattaunawa da marubucin ya yi da Sashen Hausa na Rediyon Faransa kwanakin baya, ya bayyana dalilinsa na rubuta wannan hamshaqin littafi, sannan kuma ya amsa waxansu tambayoyin daban-daban, kamar haka:
Tun yaushe ne ka fara tunanin rubuta wannan littafi na Tarihin Qasar Biu kuma me ya ja hankalinka ga aikinsa?
Masu karanta littattafan da na rubuta, za su tuna na yi xan bayani a cikin wasu littattafan, kamar wanda na yi mai suna ‘Tarihin Rubuce-Rubucena’ My Literary Journey. A ciki, na yi bayani sosai yadda na soma rubuce-rubuce, a lokacin da nake aiki kuma bayan da na bar aiki, yadda na maida hankalina wajen rubuce-rubuce har ya kai ga yau ana cewa na rubuta littattafai da yawa. Na baya-bayan nan, shi ne TARIHIN BIU, wanda ka ce ana yabawa.
To, a gaskiya, akwai tushe na wannan rubutu. A shekara ta 2006, lokacin da na kaddamar da littafi na tarihin kaina da wasu littattafan tatsuniyoyi guda biyar, sai Farfesa Muhammad Nur Alqali (Allah Ya jiqansa), shi ya yi nazari a kan littafin da na kaddamar, Hatching Hopes wanda a Hausa ake cewa Cikar Burina ke nan. Ya ce: “Ah, Malam Bukar to ga shi ka tava tarihin Biu a cikin wannan littafi, ai ya kamata ka cika, ka buga shi sosai, ka je ka nemi tarihin Biu.” Na ce ai kuwa gaskiya ne. To tun lokacin, shi ne na xauki xamara, na ce to ga shi an tada wannan zancen tarihin Biu, a gaskiya kuma na lura cewa, littafin da ya tava tarihin Biu, shi ne The Biu Book wani Baturen Mulkin Mallaka, mista J.G. Davies, D.O. (District Officer), wanda shi ne D.O. a Biu na qarshe, a shekara ta 1956 ya buga.
A yau, ba za a ce wancan littafin ga irinsa ba, domin kamfanin da ya buga shi, NORLA (North Regional Literature Agency) Zariya, to sai na lura ba a iya samunsa ma a yanzu, idan ana nema, sai ka yi bincike sosai. Ni kaina da nake nema sai da muka je laburare na Maiduguri, sai kuma mutane xaya, biyu suka samu. Na ce to, wannan gaskiya ya kamata a rubuta Tarihin Biu.
Idan ma ka lura, Turawa sun tafi a shekara ta 1960, tun lokacin can zuwa yau ai akwai tarihi. To, abin da Turawa suka rubuta bai qunshi abin da ya faru a 1960, lokacin da muka samu mulkin kai zuwa yau ba. To mun yi qoqari mu cika wannan gurbi kuma mu duba abubuwan da su Turawan suka rubuta. Akwai dai in mutum zai rubuta tarihinsa, kila wanda ka rubuta kai da kanka, wata qila zai fi sanin mutane sosai. Sai dai qarancin littattafai da muka samu, waxanda za mu duba daga baya. Amma mutane sun zo sun ba mu labarai, sun nuna mana wasu abubuwa da kwatanci.
Na duba kuma a cikin rubuce-rubuce yanzu, a halin yau, in ka tambayi mutum ko wajen Biu, tun da harshenmu na mutuwa kaxan-kaxan, ina sunan ita ce kaza? Babu. Ina sunan namun daji kaza? Babu. Ina sunan irin abinci na gargajiya. Babu. Shi ne muka yi qoqari muka ce to, wajibi a cikin tarihin Biu mu samu ban da tarihin mutane, mu tuna wa mutane sunayen itatuwa, sunayen abincin da ake yi, sunayen namun daji, sunayen tsuntsaye da hotunansu. Mutum ya ga suna kuma ya ga hoto sannan ya gan shi da Turanci da kuma in akwai, da Hausa. Amma muka ga akwai ’yar wahala wajen sunayen wasu abubuwa. To, amma dai mu mun soma, wasu suna iya qarawa.
A yanzu haka na rubuta wannan littafi, tun da ana yabawa kuma ina murna cewa mun buxe qofa ko kuma mun soma, wasu kuma su ci gaba. Idan na soma rubuta bugu na biyu, idan ya kai da yawa, za mu qara rubuta shi sai mu kawo, tare da abubuwan da mutane suka samo daga baya. Yanzu haka abin da muke ciki ke nan.
Wato duk wanda zai rubuta tarihi, kada ya wuce kai kanka da kankaa, sannan la’akari da irin rubuce-rubuce da tarihin da Turawan Mulkin Mallaka suka bari, za a tarar da cewa wani sa’in akwai kamar masu kama da almara, akwai kuma waxanda ma suka zamanto ba su da ma tushe amma duk da haka aka rungume su, ana tafiya da su haka. Wannan za a iya cewa wannan yunquri da ka yi, na ba da tarihin Biu, wanda ya qunshi xan Adam da filaye da ma tsuntsaye da kuma irin nau’in abincin da mutanen Biu ke amfani da su a wancan lokaci da ma yanayi da ake da shi, na rani, na damina, na iska da dai makamantansu; yana nuna kamar wani juyin-juya-hali na sake dawo da gyara kura-kuren wataqila da aka rubuta a tarihin mutane waxanda ya zamanto yanzu su da kansu a yanzu sun dawo sun rungumi abinsu?
To, a gaskiya ban soma rubuta tarihin Biu saboda in gyara wasu abubuwan da Turawa suka yi ba. Ni dai su xin ma sun ce akwai lokacin da zai zo, wanda ’yan qasa za su rubuta tarihinsu. Wannan sun faxa a lokacin, a cikin littafin da J G. Davies, wanda ya rubuta tarihin Biu, The Biu Book ya yi nazari a kan cewa, akwai fa lokaci zai zo, wanda ’yan qasa za su rubuta tarihin su. To kuma gaskiyar haka ta bayyana, domin ga shi lokacin ya zo; shi ne kuma yanzu muka rubuta.
Turawa, kamar su mishan da na mulki na Birtaniya, sun yi rubutun wasu abubuwa saboda su samu hankalin mutanen da suke mulka, shi ya sanya suka je suna binciko tarihi domin su sani. Domin ma damar kana son ka samu kan mutum, dole ka nemi yadda tarihinsa yake. Shi ya sanya suka nemi yadda za su sha kan mutanen da suke mulki a kansu. Wannan shi ne babban dalilin da ya sanya suka rubuta tarihinsu da tatsuniyoyi, domin in ka san yadda mutum yake, za ka gane yadda abubuwa suke a tare da shi.
Mun sani akwai qalubale kuma ba a xan qaramin lokaci ba ne, za a ce an rubuta tarihi wanda zai kasance ingantacce kuma ya samu karvuwa ga jama’a, sai an yi karatun-ta-natsu, ma’ana sai an xauki lokaci mai tsawo kamar yadda muka gani a littafinka na Tarihin Biu, wajen kusan shekaru tara, kafin ma ka kammala shi ya fito. Shin wane irin qalubale da kuma irin wahalhalu ka fuskanta wajen rubuta wannan littafin ko kuma al’amarin Allah, abin ya zo maka a cikin sauqi?
Al’amarin, Allah Ya kawo mani shi a cikin sauqi. Wallahi sai bayan da na gama littafin, sannan na duba na ga lallai ashe abin har ya kai shekara takwas da rabi zuwa tara, abin da muka soma a shekara ta 2006; Allah Ya ba mu tsawon rai har ya kai ga shekara ta 2015 zuwa 2016. To, babu wani qalubale, in dai mutum ka sa kanka a kan wani aiki; za ka samu nasara kuma Ubangiji Ya ba ni tsawon rai na ga wannan. Ba safai ba ne wani ya fara wani abu, ya xauki wannan tsawon lokaci, a ga bayansa.
A gaskiya waxanda muka soma da su ma, idan na qirga wasu xaya, biyu, uku, wasu sun rasu, a tsakanin lokacin da muka soma wannan bayani. Saboda haka ni kam ina gode wa Allah kuma waxanda suka taimaka, idan ka duba a cikin littafin, za ka ga xaya, biyu, waxanda suka rasu a lokacin kuma akwai waxanda na ambaci sunansu, waxanda suka taimake ni a ciki da yawa, har yanzu suna da rai. To Allah Shi Ya taimaka mana muka samu nasara, kowa ya ga abin da suka yi.
Wasu, su suka ce, ai ashe a lokacin da muka gani, ai ba mu xauki abin kamar haka ba, sai da littafin ya fita. Wasu ma da suka so su ba da labari amma suka ja baya, yanzu suna cewa da-na- sani. Shi ne suke cewa, don Allah idan za ka buga littafi na biyu, yanzu muna da wasu labaru da bayani tsantsa, waxanda za mu iya mu ba ka. Na ce, to Alhamdu lillahi, a yanzu haka dai mun gode wa Allah.
Babu wani qalubale wajen haxa wannan tarihi na Biu. Wajen tunani na mutane, tun da abin adabin baka ne, wasu za su iya mantawa amma na lura cewa akwai tsofaffi da yawa, har yanzu qwaqwalwarsu, waxanda masu shekaru casa’in suna da rai, suna tunawa da tatsuniyoyi da wasu labarun abubuwan da suka faru, wallahi za ka yi mamaki. Za ka ga kamar qwaqwalwar… wace dabba ce mai qwaqwalwar nan sosai? To mutane, akwai wasu mata da maza haka da dama da suka taimaka wajen tarihi.
Wato masu qwaqwalwan alhudu-hudu ke nan ko na aku?
E, da giwa.
Wannan aiki da ka ce Allah Ya kawo cikin sauqi tare da taimakon wasu da suka riga suka mutu, wannan yana nufin cewa tun da aka fara rubuta wannan littafin cikin shekaru takwas ba a dakatar ba, ana ci gaba da neman bayanai har lokacin da ya kammalu ne ko kuwa akwai wani lokaci da aka dakatar? Kuma gungun mutane ne ka tara, waxanda suka kula da taimaka maka ko kuwa?
Wallahi ba zan iya tuna cewa tun lokacin da muka soma mun tsaya ba. Ni dai na xauka tarihi abu ne na kai-kawo, idan ka samu wani labari dole sai ka qara bincikawa. To wajen kai-kawo muka samu wannan labari sai mu qara zuwa, muna qara tambayar mutane, haka ne ko ba haka ba? Sannan muka rubuta, kuma lokacin da na gama rubutawa sai da na tura wa mutane kamar 40, vangarori daban-daban na ’yan Nijeriya. Wajen Yarabawa ne ko wajen Ibo da sauran wurare, duk na tura wa mutane, suka dudduba suka qara kawo mani gyare-gyaren da suka yi. Saboda haka, wannan jiran na xan lokaci mutane su ba da ra’ayinsu, bayan da muka tattara littafin mai yawa.
Ashe dai rubuta littafin tarihi ba qaramin aiki ba ne?
In za ka rubuta littafin labarin qirqire, kana iya ka zauna gida ka fitar da littafi amma dai na tarihi, ra’ayi ne amma ban da ra’ayi za ka fa rubuta labarin mutane ne, don haka sai an yi a hankali kuma, za ka lura ba jaddawali ba ne, idan an ce biyu da biyu, ka ce huxu; a’a. Littafin tarihi dole sai ka qara dubawa, a qara dubawa, a kai wa mutane a duba, a tantance. Shi ne abin da muka yi ke nan, rubuta littafin tarihi daban da na qirqira.
Wannan aiki da ka yi, idan aka lura da girmansa da kuma yadda ya samu yabo, ba ma tarihin Biu ba, littattafanka da dama suka sa har ma Jami’ar Ahmadu Bello ta ga cewa kai, aikin da kake yi ya kamata ta karrama ka; idan muka xauka, Doktan Adabi da ta xauka ta ba ka a shekarar da ta gabata. Bayan haka kuma akwai yabo da dama daga hukumomi daban-daban. Wannan aiki na tarihi, wasu za su tambayi kansu cewa, ai gwamnati ya kamata ta xauki nauyin yin irin wannan aiki amma sai ga shi kai ka riga ka xauka. Da ka xauka yanzu, yaya za a yi da littafin? Za ka haxa da gwamnati ne ko kuwa ya lamarin yake?
A’a, gaskiya abin da na gani da littafin, da mutane suka karanta, ra’ayin da suka faxa shi ne ya faranta mani rai. Na ga mutane suna baqin ciki cewa, da suka karanta wannan littafi, suka ce yaya ne gwamnati ta je ta soke tarihi a cikin al’amarin manhajar makaranta? Mutane suka ce in ba ka san makomarka ba, ba ka san inda ka tashi ba, ina za ka san inda za ka nufa a gaba? Wannan ya nuna cewa mutane suna neman tarihi, ko ba namu ba, na qasashe ko na wa ne. Dole mutum ya san tarihin inda ya taso kuma shi ne zai ba shi haske ta inda zai je ya nufa. Mutane da yawa waxanda suka ba ni ra’ayinsu a kan wannan littafi sun ce wallahi kuskure ne gwamnati ta yi da ta soke tarihi a cikin manhajar makaranta.
Za mu ci gaba