✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buratai ya soke taron shekara bayan soja ya kamu da COVID-19

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta Rufe Babban Taronta na 2020 bagatatan, bayan da wani hafsanta da ke halartar taron ya kamu da cutar COVID-19.…

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta Rufe Babban Taronta na 2020 bagatatan, bayan da wani hafsanta da ke halartar taron ya kamu da cutar COVID-19.

Shugaban Rundunar, Laftanar Janar Tukuar Buratai ya sanar da soke ragowar abubuwan da a yi a taron da ofishinsa ke gudanarwa a duk shekara, don guje wa yaduwar cutar.

“Sakamakon sake bullar cutar COVID-19 a Abuja a karo na biyu da kuma kamauwar daya daga cikin hafsoshin da ke halartar taron Shugaban Rundunar Sojin Kasa na 2020; An soke ragowar abubuwan da aka shirya a taron”, inji kakakin rundunar, Birgediya Sagir Musa.

Rundunar ta kuma umarci mahalarta taron da su killace kansu na tsawon kwana 14 tare da kiyaye sauran matakan kariyar cutar a tsawon lokacin domin tabbatar da yanayin lafiyarsu.

“An umarci dukkanin mahalarta taron da su killace kansu kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta tsara domin kauce wa yaduwar COVID-19”, inji sanarwar ta ranar Alhamis 10 ga watan Disamba, 2020.

An fara taron wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bude ne a ranar Litinin.

Buhari da sauran shugabanni sun halarcin taron ne ta bidiyo yayin da Mininstan Tsaro, Bashir Magashi, Buratai da sauran shugabanni suka hallara a zauren taron.