Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta bude babban sansani domin yakar ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a yankin Faskari na Jihar Katsina.
Yayin kaddamar da sansanin, Babban Hafsan Rundunar, Laftanar Janar Tukur Buratai ya ce sansanin zai mayar da hankali ne wajen yakar ‘yan bindiga da dangoginsu da ke addabar al’ummomin yakin Arewa-maso-Gabas.
- ‘Yakin Najeriya a Laberiya ne silar rashin tsaro a teku’
- Matsalar tsaro: Obasanjo ya bukaci a sauya tsarin Najeriya
“Za a kaddamar da yyukan dauki a daukacin sassan kasar nan guda shida a tare domin kyautata alaka tsakanin sojoji da fararen hula”, kamar yadda ya ce.
Ya ce sansanin da ire-irensa a sauran yankunan na daga abubuwan da aka tsara na bikin Ranar Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya na bana (NADCEL 2020) wanda ya kunshi fara aikin soji na musamman, ‘Exercise Sahel Sanity’, domin nuna karfin rundunar na yakar miyagun laifuda a fadin Najeriya.
Sai dai ya ce bikin na bana bai hada da bangaren tunawa da ‘yan mazan jiya ba saboda cutar coronavirus, amma za a yi kyakkyawan tanadin yin sa bayan lafawar cutar.