✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buratai ya bude hanyar Maiduguri zuwa Damboa bayan an rufe ta wata 13

Babban Hafsan Sojin Kasa Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai yau Talata ya sake bude babbar hanyar Maiduguri zuwa Damboa, tun bayan rufe hanyar kimanin wata…

Babban Hafsan Sojin Kasa Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai yau Talata ya sake bude babbar hanyar Maiduguri zuwa Damboa, tun bayan rufe hanyar kimanin wata 13 sakamakon barazanar rashin tsaro.

Buratai, ya bayyana cewa an bude hanyar ne a shingen binciken ababen hawa da ke Molai da ke wajen birnin Maiduguri a jihar Borno.

A yanzu haka matafiya zasu iya amfani da hanyar da ke tsakanin Maiduguri zuwa Biu da kuma wasu unguwanni da suka hade garuruwan yankin.

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, ne ya bukaci da bude hanyoyin lokacin da ya ziyarci Ministan tsaron Najeriya Bashir Magashi.