✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bullar kwalara a sansanin ’yan gudun hijirar Jihar Borno

Kimanin makowanni biyu kenan da aka samu labarin bullar cutar kwalara a sansanin ’yan gudun hijira da ke sassan Jihar Borno.  A rahoton da Majalisar…

Kimanin makowanni biyu kenan da aka samu labarin bullar cutar kwalara a sansanin ’yan gudun hijira da ke sassan Jihar Borno.  A rahoton da Majalisar dinkin Duniya ta fitar an nuna cutar ta kama wadanda ke zaune ne a sansanonin ’yan gudun hijira su kimanin 530 inda 23 daga ciki suka mutu.  Sashen bayar da agaji na Majalisar dinkin Duniyar ya ce cutar kwalarar ta fara bulla ne a ranar 16 ga watan Agustan wannan shekara a sansanin ’yan gudun hijirar amma ganin yadda ta rika yaduwa tamkar wutar daji  ya zuwa ranar 5 ga watan Satumba ta kama mutum 530 kuma 23 daga ciki sun mutu.

Cutar ta fi tsanani ne a sansanin ’yan gudun hijira na Muna Garage da ke kunshe da masu gudun hijira su kimanin dubu 20.  Sannan an samu labarin bullar cutar a sansanonin ’yan gudun hijira na Custom House da Ruwan Zafi da kuma na Bolori II da ke kusa da sansanin masu gudun hijira na Muna Garage.  Sannan rahoton ya ce an samu bullar cutar a kananan Hukumomin Monguno da na Dikwa.

Masana harkar kiwon lafiya sun danganta bullar cutar ne a kan ruwan saman da aka rika tafkawa kamar da bakin kwarya na kwana da kwanaki.  Hakan kuma ba ya rasa nasaba da irin yadda ake yi wa ’yan gudun hijirar rikon sakainar kashi na rashin ba su kulawar da ta dace.

A gaskiya mun yaba game da rahoton da Majalisar dinkin Duniya ta fitar a game da bullar cutar a sansanin ’yan gudun hijirar.  Hakan ya taimaka wajen janyo hankalin hukumomin da abin ya shafa wajen kai musu agajin gaggawa.  Sannan mun yaba da matakin da gwamnatin Jihar Borno da Hukumomin bayar da agajin gaggawa suka dauka game da kai wa ’yan gudun hijirar dauki.  Sai dai muna kira da a kara inganta harkar kiwon lafiya a sansanin musamman wajen samar musu da tsaftataccen ruwan sha da kuma dakunan ba-haya.  Haka kuma gwamnati ta yi kokarin samar da magudanun ruwa a sansanin da kuma hana su zuba shara barkatai don a tserar da su daga kamuwa daga cututtuka.  Sannan a hori ’yan gudun hijirar daga yin ba-haya a fili.

Ya dace a rika tura jami’an kula da kiwon lafiya zuwa sansanin ’yan gudun hijirar duk  a kokarin shawo kan bullar cutar ta kwalara. Haka kuma ya dace gwamnati ta samar musu da isassun magunguna don yakar cutar.

A game da batun mayar da ’yan gudun hijira gidajensu na asali kuwa, gwamnati ta mayar da hankali a game hakan, don hakan zai taimaka sosai wajen shawo kan bullar cutar.

Ya kamata gwamnatocin jihohi su rika samar da magudanun ruwa ga al’umma.  A kwanakin baya ne aka samu ambaliyar ruwa a Jihohin Kogi da Benuwe.  Yakamata gwamnatocin wadannan jihohi su dauki mataki don kare al’ummar jihohin daga kamuwa daga cutar kwalara.  Matakin farko shi ne su tabbatar sun tsaftace sansanin da za a tsugunar da wadanda ambaliyar ta shafa.

Yana da kyau a rika fadakar da al’umma muhimmancin yin tsafta da kuma kula da lafiya, don kwalara ta fi shafar wuraren da suke da kazanta ne.  Sannan a rika daukar isassun jami’an kula da kiwon lafiya wadanda za su rika fadakar da al’umma muhimmancin kula da kiwon lafiya kuma a ba zu karfin ikon hukunta duk mai zubar da kazanta a bainar jama’a ba tare da wani dalili ba.

 Abin takaici ne ganin yadda jihohi da dama ba su da motocin kwashe shara.  Sannan yakamata gwamnati da hukumomi su shiga wayar da kan al’umma muhimmancin kula da lafiya da kuma shan ruwa mai tsafta musamman mazauna karkara.  Ya dace gwamnati ta dauki matakin kawar da cutar kwalara, don kauce irin bala’in da ya faru a farkon shekarar nan da muke ciki inda cutar sankarau ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 1,114 a kasar nan. 

Muna kira ga gwamnatoci a kowane mataki su dauki matakin gaggawa don ganin an shawo kan bullar cutar kwalara a kasar nan.