✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari zai yi wa ’yan Najeriya jawabi ranar Juma’a

Jawabin, wanda zai kasance na sabuwar shekara ne za a watsa shi da misalin karfe bakwai na safe.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi wa ’yan Najeriya jawabi ranar Juma’a, daya ga watan Janairun 2020.

Jawabin, wanda zai kasance na sabuwar shekara ne za a watsa shi da misalin karfe bakwai na safe.

Babban Mai Taimakawa Shugaban Kan Harkokin Watsa Labarai, Malam Garba Shehu shine ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis

Shehu ya umarci dukkan kafafen watsa labaran gwamnati na rediyo da talabijin su hada ta tashoshin FRCN da NTA domin watsa jawabin kai tsaye.