A ranar Talatar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai karbi bakuncin jiga-jigan jam’iyyar APC a fadarsa da ke Abuja inda za su yi buda-baki tare.
Rahotanni sun ce wadanda aka gayyata sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma mai neman takarar Shugaban Kasa, Bola Tinubu, tsohon Shugaban APC na kasa, Dr John Oyegun, Adams Oshiomhole da kuma tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Murtala Nyako.
- Yahaya Bello ya zama dan takarar da ya fara sayen fom din APC a kan N100m
- Rarara da mawakan 13×13 sun yi waka kan matsalar tsaro
Sauran sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Olusegun Osoba, tsohon Shugaban APC, Bisi Akande, tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu-Sheriff, tsohon Gwamnan Zamfara, Ahmed Sani Yarima, tsohon Gwamnan Sakkwato, Aliyu Wamako, sai kuma tsohon Gwamnan Edo, Oserheimen Osunbor.
Haka nan, akwai tsohon Gwamnan Yobe, Bukar Ibrahim, Janar Muhammed Magoro, Sanata Lawal Shuaibu, Sanata Abba Aji, Sanata Tijjani Tumsah, Sanata Fati Bala, Sanata Abubakar Guru, da kuma Sanata Nasiru Danu.
Wannan na kunshe ne cikin wasikar gayyata mai dauke da kwanan watan 22 ga watan Afrilun 2022 tare da sa hannun Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, da aka aike wa shugaban APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu.
Gambari, a cikin wasikar ya ce, “Na rubuta wannan wasika ne domin sanar da kai cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a isar da gayyatarsa ga jerin jagororin APC da sunayensu ke hade da wasikar, domin su zo su yi buda-baki tare da Shugaban Kasa a ranar Talata, 26 ga Afrilu, 2022, da misalin karfe shida da rabi na yamma a Zauren Taro na Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
“Da wannan ake bukatar ka gayyato wadanda lamarin ya shafa. Ana bukatar mahalartan su isa ‘Pilot Gate’ da karfe 4:30 na yamma don yi musu gwajin COVID-19, kana su isa zauren taro da karfe 6:00.”