Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba zai bar Abuja zuwa Banjul babban birnin kasar Gambiya, don halartar bikin rantsar da Shugaba Adama Barrow bayan sake lashe zabe da ya yi a karo na biyu.
Garba Shehu, hadimin Shugaban Kasa kan kafafen watsa labarai ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Talata.
- Buhari bai taba ba da umarnin janye tallafin mai ba — Lawan
- Direbobin motocin haya za su fara biyan harajin N292,000 duk shekara a Legas
Ya ce Shugaban zai samu rakiyar Ministan Harkokin Kasashen Waje, Mista Geoffrey Onyeama, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkar Tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno, Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ambasada Ahmed Rufa’i da sauran manyan jami’an Gwamnatin Tarayya.
Garba Shehu, ya ce Buhari zai zama bako na musamman daga cikin manyan bakin da aka gayyata a wajen bikin rantsar da Shugaba Barrow da za a yi a filin wasa na Bakau.
Ya ce Shugaba Buhari da sauran manyan shugabannin ECOWAS sun taka muhimmiyar rawa wajen daidaita al’amura da samar sa zaman lafiya a kasar a 2017, lokacin da tsohon Shugaban Kasar, Yahya Jammeh ya ki mika mulki bayan faduwa zabe.
Hadimin ya ce ana sa ran Buhari zai dawo Abuja da zarar an kammala bikin rantsuwar.