Shugaba Buhari zai kai ziyar aiki kasar Portugal inda za a karrama shi da lambar giramamawa da ta fi kowacce a kasar.
Fadar Shugaban Kasa ta ce Buhari zai kai ziyarar ce a ranar Talata, bayan Shugaba Marcelo Rebelo de Sousa ya gayyace shi domin su tattauna wasu muhimman batutuwa da suka shafi kasashen.
- Ba za mu yi wa zabin ‘yan Najeriya katsalandan ba a 2023 – INEC
- Dan sanda ya bindige direban tirela a Binuwai saboda ‘na goro’
Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya ce a lokacin ziyarar, za a ba wa Buhari lambar girmamawa mafi girma a kasar Portugal, wato ‘Great Collar of the Order of Prince Henry.’
A lokacin ziyarar Buhari da Shugaba Marcelo Rebelo de Sousa za su jagoranci taron kasashen biyu, gami da sanya hannu kan yarjejeniya kan wasu batutuwa.
Buhari zai kuma ziyarci majalisar dokokin kasar, inda zai gana da Shugaban Majalisar Dattawa, Dokta Augusto Santo Silva da kuma Fira Minista Antonio Costa.