Gwamnatin Tarayya ta amince da jinginar da tashar jiragin ruwa ta Badagry da ke Jihar Legas ga ’yan kasuwa kan kudi sama da Naira tiriliyan daya.
Gwannatin ta amince da hakan ne a taron Majalisar Zartarwa ta Kasa za ta sayar da tashar ne a kan kudi kimani Naira tiriliyan 1.076.
- An hana ’yan wasa ‘durkusa gwiwoyi a kasa’ kafin fara wasanni a gasar Firimiya
- Matar da mijinta ya buya a ban-daki saboda ’yan fashi ta bukaci a raba aurensu
A bisa tsarin dai, ’yan kasuwa za su gina ta, su kuma gudanar da ita har tsawon wani lokaci sannan su dawowa da gwamnati ita.
Ministan Sufuri, Mu’azu Jaji Sambo ne ya sanar da hakan, a bayan taron Majalisar Zaratarwa ta Kasa wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a Abuja Fadar Shugaban Kasa ranar Laraba.
Sambo ya ce ’yan kasuwar za su rike wurin har tsawon shekara 45, tare da sa ran za su samar da kudin shiga na kimanin Dala biliyan 53.6.
Sannan Ministan ya kara da cewa, “A karkashin wannan tsari, ’yan kasuwa za su sa kudinsu tare da gina wurin, su kuma gudanar da shi, bayan wa’adin da muka amince za su dawowa da Gwamnatin Tarayya da tashar ta hannun Hukumar Kula da Tasoshin Jiragen Ruwa ta Kasa (NPA).”
Ana sa rai gina tashar zai samar da aikin yi ga mutane 250,000, zai kuma janyo wa kasar musu zuba jari daga kashen waje wanda hakan taimaka wa tallatin arzikin Najeriya baki daya.