Shugaba Muhammad Buhari zai kai ziyarar aiki kasar Saudiyya ranar Litinin, domin halartar taron zuba jari.
Sanarwar Fadar Shugaban Kasa ta ce bayan kammala taron zuba jarin na kwana uku, wanda zai gudana a birnin Riyadh, Shugaba Buhari zai zarce zuwa birnin Makkah, inda zai yi Umrah kafin ya dawo Najeriya ranar Juma’a.
- Saudiyya: Sarki Salman ya sa a kara wa’adin zaman baki kyauta
- Buhari sam ba ya nema ko daukar shawara —Ghali Na’Abba
Manyan ’yan kasuwa, masu masana’antu da kwararru a fannin banki da man fetur daga Najeriya na daga cikin mahalarta taron da zai mayar da hankali kan zuba jari domin nan gaba a duniya.
Mahalarta taron daga Najeriya sun hada da: Alhaji Aliko Dangote, Alhaji Mohammed Indimi, Alhaji Abdulsamad Rabiu, Hassan UsmanTope Shonubi, Wale Tinubu, Alhaji Abdulsamad Rabiu, Hassan Usman, Omoboyode Olusanya, Abubakar Suleiman, Herbert Wigwe da Leo Stan Ekeh.
Jami’an gwamantin da za su yi wa Buhari rakiya sun hada da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami; Minista a Ma’aikatar Man Fetur, Timipre Sylva, Minista a Ma’aikatar Harkokin Waje, Zubairu Dada, da Shugabar Hukumar Kula da ’Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje, Abike Dabiri-Erewa da sauransu.