Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai bar Najeriya a ranar Alhamis din nan zuwa kasar Jamhuriyyar Nijar domin halartar taron tattalin arziki na Kungiyar Tarayyar Afirka (AU).
Fadar shugaban kasa ta sanar a ranar Laraba cewa a lokacin taron, Buhari zai gabatar da jawabi, sannan ya halarci wani taron kaddamar da fassarar littafin da aka yi a kansa, wanda aka fassara zuwa harshen Faransanci.
- ’Yan Najeriya 7 da ke wakiltar wasu kasashen a Gasar Kofin Duniya
- NAJERIYA A YAU: Shin gwamnonin G5 za su iya hana Atiku cin zabe?
Sanarwar da hadimin shugaban kasa Garba Shehu, ya fitar ta ce, “Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki birnin Niamey, hedikwatar kasar Nijar domin halartar Babban Taron Kungiyar Tarayyar Afirka kan Masana’antu da Fadada Tattalin Arziki.
“Zai kuma halarci zaman da za a yi kan Yarjejeniyar Kasuwanci Maras Shinge Tsakanin Kasashen Afirka (AfCFTA).”
Ya kara da cewa shugaban, wanda zai tashi daga Abuja a ranar Alhamis 24 ga Nuwamba, 2022, “Zai kuma kaddamar da wani titi da Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanya wa sunansa, ‘Titin Muhammadu Buhari’.
Ya je gabanin taron na AU Buharin zai halarci taron kaddamar da fassarar Faransanci na littafin ‘Muhammadu Buhari: Kalubalen Shugabanci a Najeriya’ (Muhammadu Buhari: The Challenges of Leadership in Nigeria).
Wani malamin Nazarin Harkokin Kasashe a Jami’ar George Mason da ke Arewacin Virginia a kasar Amurka, Farfasa John Paden, ne mawallafin littafin.