A wani mataki na kara nesanta kanta da Faransa da ta yi mata mulkin mallaka, Nijar ta ayyana harshen Hausa a matsayin yaren ƙasa a madadin Faransanci.
Kamfanin dillancin labarin kasar AFP ne ya ruwaito hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 31 ga Maris.
- Boko Haram na sake ƙwace ikon wasu yankuna a Borno — Zulum
- Ma’aikatar Jin-ƙai ce kan gaba wajen wawure kuɗin gwamnati — Tsohon Minista
Tun bayan hambarar da gwamnatin farar hula ta Muhammad Bazoum, Nijar ɗin ke ɗaukar matakan nesanta kanta da Faransa, inda ta fara da korar sojojinta da kuma sauyawa wurare da dama da ke da alaƙa da kasar suna.
Bayan haka kuma, Nijar ɗin da sauran ƙasashen da Faransan ta yi wa mulkin mallaka da suka haɗa da Mali da Burkina Faso suka fice daga Kungiyar Ƙasashe Rainon Faransa (OIF), wacce take tamkar ƙungiyar ƙasashen rainon Ingila wato Commenwealth.
Matakin dai wani ɓangare ne na sakamakon taron ƙasar da aka gudanar a watan Fabrairu, wanda ya bayar da wa’adin shekaru biyar ga mulkin sojin da Janaral Abdourahamane Tiani ke jagoranta.
Hausa ne yaren da aka fi magana da shi a ƙasar, musamman ma a Zinder da Maraɗi da ke tsakiya maso kudanci, da kuma a Tahoua da ke yammaci.
Haka kuma, kimanin kashi 13 na jama’ar Nijar na magana da yaren Faranshin ne, ko kuma dai sama da mutum miliyan uku. kamar yadda sanarwar ta bayyana.