Gwamnatin Jihar Kogi ta ayyana ranar Alhamis a matsayin hutu, saboda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar kaddamar da aiki a Jihar.
Gwamnatin ta ce Buhari zai kai ziyarar ce don bude wasu ayyuka da Gwamnan Jihar, Yahaya Bello ya kammala.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kan Ranar Kyauta A Addinin Kirista
- Mutum 5 sun mutu a fadan kabilanci ranar Kirsimeti a Delta
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Kingsley Fanwo, ya fitar a ranar Lahadi a Lokoja, babban birnin Jihar.
“Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Muhammadu Buhari, GCFR, zai ziyarci Jihar Kogi a ranar 29 ga watan Disamba, 2022 domin kaddamar da wasu ayyuka.
“Saboda haka, Gwamna Yahaya Bello ya ayyana ranar ta Alhamis, 29 ga watan Disamba, 2022 a matsayin ranar hutu,” inji sanarwar.
Gwamnatin jihar ta bukaci al’ummar da su yi fitar farin dango don tarbar Shugaba Buhari.
Kazalika, Gwamnatin ta bukaci kungiyoyin kwadago da masu zaman kansu da jami’an tsaro su tabbatar da zaman lafiya ya wakana a yayin ziyarar ta Buhari.
Buhari dai na ci gaba da ziyartar jihohin Najeriya don kaddamar da ayyuka.