Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai mika wasu karin jiragen saman Shugaban kasa ga Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya baya ga biyun da aka sanya a kasuwa, kamar yadda fadar Shugaban kasa ta bayyana a makon jiya.
Yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban kasar kan Harkokin Watsa Labarai Malam Garba Shehu, ya ce daga cikin jiragen Shugaban kasar akwai wadanda ake ganin za su yi amfani ga Rundunar Sojojin Saman kuma za a aika mata da su.
“Ana sa ra nan da ’yan kwanakin da ke tafe Kwamandan da ke Kula da Jiragen Sama na Fadar Shugaban kasa zai hadu da Babban Hafsan Sojojin Sama na Najeriya domin mika masa wadannan jirage,” kamar yadda Garba Shehu ya bayyana wa gidan rediyon BBC, Landan.
Rage yawan jiragen da Shugaban kasa ke amfani da su dai na daga cikin alkawurran da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kafin hawansa mulki a bara domin yin tsimin kudin da ake kashewa wajen kula da su.
Amma kuma Shugaban ya ci gaba da amfani da jirage fiye da 10 da ya gada daga tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan fiye da tsawon shekara daya; sai ranar Talata lokacin da aka sanar da matakin sayar da biyu daga cikinsu da kuma na mika wasu da ba a ambata ba ga sojin sama.
Buhari zai ba sojojin sama wasu jiragensa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai mika wasu karin jiragen saman Shugaban kasa ga Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya baya ga biyun da aka…