Ooni na Ife, Mai martaba Oba Adeyeye Ogunwusi, a ranar Alhamis ya yaba wa Muhammadu Buhari bisa ƙoƙarin da ya yi a lokacin da yake shugabancin Nijeriya.
A wata sanarwa da manema labarai suka samu, Sarkin ya bayyana hakan ne a ziyarar kwanaki biyu da ya kai wa tsohon shugaban ƙasar a gidansa da ke Daura a jihar Katsina.
- Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗin 2025 ga Majalisa ranar Talata
- Abba ya sauke Sakataren Gwamnatin Kano da Kwamishinoni 5
Sanarwar ta ce, ziyarar ta ba da damar tattaunawa mai ma’ana tsakanin Mai Martaba Sarkin da tsohon shugaban ƙasar kan muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban Nijeriya.
Da yake bayyana jin daɗinsa, Oba Ogunwusi ya bayyana cewa Buhari ya nuna matuƙar farin ciki a ganawar ta su.
Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, a ranar Alhamis, ya yaba wa Muhammadu Buhari bisa ƙoƙarin da ya yi a lokacin da yake shugabancin Nijeriya.