✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya yi Allah wadai da harin Kaduna

Shugaba Buhari ya fusata tare da yin Allah yinwadai game da harin Kaduna.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da sabon harin da ’yan bindiga suka kai a Jihar Kaduna.

Shugaban Kasar, cikin wata sanarwa da hadiminsa kan kafafen watsa labarai, Garba Shehu, ya fitar ya ce farmakin da aka kai yankin Kauran Fawa, Marke da Ruhiya da ke gundumar Idasu a Karamar Hukumar Giwa ya fusata shi.

Cikin mako guda ’yan bindiga sun kashe mutane da dama a yankunan Kananan Hukumomin Zangon Kataf, Chikun, Birnin Gwari, Igabi da kuma Kauru duk a jihar Kaduna.

Shugaba Buhari ya jajanta tare da aike da ta’aziyyarsa ga daukacin al’ummar Najeriya da kuma jama’ar kabilar Zonkwa kan rasuwar shugabansu, Agwan Bajju, Nuhu Bature, wanda ya yi wa fatan samun rahama ga mamacin.

Ya ce jami’an tsaro na kan aikinsu na ganin sun dakile ayyukan ’yan bindiga wadanda suka addabi mutanen da ba su ji ba, su gani ba, wajen kashe su da kuma kone musu muhallai.

Kazalika, ya ba wa jami’an tsaro umarnin bankado maboyar ’yan bindiga tare da yi musu magana da yaren da suka fi fahimta.