✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya tura sojoji don kubutar da Daliban Kagara

Ya umarce su da su tabbata su kubutar da daliban da sauran mutanen cikin hanzari

Shugaba Buhari ya tura sojoji da ’yan sanda domin su kubutar da dalibai da ma’aikatan Kwalen Kimiyya ta Gwanatin Tarayya da ke garin Kagara, Jihar Neja da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Ya umarce su da su tabbatar su kubutar da daliban da sauran wadanda aka yi garkuwa da su a makarantaa ba tare da bata lokaci ba.

“Bayan samun rahoton, Shugaba Buhari ya umarci sojoji da ’yan sanda cewa su tabbata sun ceto duk wandanda aka yi garkuwar da su cikin hanzari.

“Ya kuma tura manyan jami’an tsaro zuwa Jihar Neja inda za su gana da jami’an gwanatin jihar da shugabannin al’umma da kuma iyayen dalibai da ma’aikatan kwalejin,” inji Fadar Shugaban Kasa.

Yadda aka yi garkuwa da mutane a Makarantar Kagara

Da misalin karfe biyu na dare ranar Talata ne ’yan bindiga suk kai hari Kwalejin Kimiyya ta Gwamnatin Tarayya da ke garin Kagara a Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja.

Maharan sun rika bi gidajen ma’aikata dakunan kwanan dalibai sannan suka tara su a wuri guda sannan suka yi cikin jeji da su zuwa inda ba a sani ba.

Wani shaida ya da maharan sun bindige wani dalibi da ya yi yunkurin tserewa a lokacin da suka kai harin da talatainin dare.

Jami’an tsaro sun gana da mahukunta

Tuni jami’an tsaron da za su jagoranci aikin ceton suka gana da jami’an Gwamnatin Jihar Neja da shugabannin al’umma da kuma iyayen dalibai da jami’an makarantar.

“Shugaban Kasa ya kuma ba wa sojojin tabbacin samun cikakken goyon bayansa sa jan aikin da suke yi na yaki da ta’addanci da ’yan bindiga, yana mai cewa su yi duk mai yiwuwa wajen shawo kan lamarin tare da kawo karshen hare-hare a kan makarantu a nan gaba.

“Muna taya iyalan wanda aka yi garkuwa da su din addu’a,”inji sanarwar da kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba.

An yi garkuwa da mutum 42 a makarantar Kagara

Da tsakar dare ne dai mahara suka kai hari makarantar suka rika bi gidan ma’aikata da dakunan kwanan dalibai inda suka yi garkuwa da mutum 42.

Sa’o’i kadan bayan an yi garkuwar, Gwamna Abubakar Sani Bello na Jihar Neja ya rufe makarantun sakandaren kwana nan take a Kananan Hukumominta hudu har sai abin da hali ya yi.

Ya bayyana cewa wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da dalibai 27 da ma’aikata 27 da kuma iyalansu mutum 23.

Kananan Hukumomin da aka rufe makarantun kwanan su ne Rafi da Munya da Mariga da kuma Shiroro.

Gwamnan ya yi kira ga al’umma da su taimaka da duk wani bayani da za su taimaka wajen ceto daliban da sauran wadanda aka yi garkuwa da su.

Wadanda aka sace

Hukumomin makarantar na ci gaba da daukar bayanan wadanda suka rage a makarantar domin tantance adadin wadanda da aka yi garkuwa da su.

Wata majiya ta ce daya daga cikin ma’iakatan makarantar ya samu ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Ta ce wandada aka yi karguwa da su sun hada da Lawal, Ali, Hannatu  tare da mijinta, Dodo, da kuma Mohammed Abubakar(Akawu).

Tuni dai jami’an tsaro suka bazama bin sawun ’yan bindigar yayin da jirgin soji ke ta shawagi a sararin samaniya domin gano inda maharan suka yi da daliban da malaman.