✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya taya Tinubu murnar shugabancin ECOWAS

Daga Muideen Olaniyi Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya shugaba Bola Tinubu murnar zaɓensa da aka yi a matasyin shugaban bunƙasa arzikn Afirka ta…

Daga Muideen Olaniyi

Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya shugaba Bola Tinubu murnar zaɓensa da aka yi a matasyin shugaban bunƙasa arzikn Afirka ta Yamma (ECOWAS)

Kakakin tsohon shugaban, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a sanarwar da ya rabawa manema labarai.

Ya ce “Al’ummar Afirka ta Yamma sun damƙawa sabon shugabanmu gagarumin aiki don haka aikinmu a matsayinmu na ƴan ƙasa mu taimaka masa don ganin bai bada kunya ba.”

Tinubu ya zama sabon Shugaban ECOWAS

ECOWAS ta damu da yadda kasashe ke kunnen uwar shegu da hukuncinta

Ya ƙara da cewa ‘Ina fatan Ubangjiji zai sa a farfaɗo da ECOWAS a matsayin ƙungiyar tabbatar da dimokraɗiyya, kyakkyawan shugabanci, da yaki da ta’addanci da sauyin muhalli a zamanin mulkinsa.”