✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ECOWAS ta damu da yadda kasashe ke kunnen uwar shegu da hukuncinta

Sai dai ECOWAS ta ce za ta ci gaba da tabbatar da komai na tafiya daidai a kungiyar.

Shugaban Kotun Kungiyar Bunkasa Tattalin Arziki Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), Mai Sharia Edward Amoako Asante, ya nuna takaicinsa kan yadda kasashe mambobin kungiyar ba sa aiwatar da hukuncin da kotun ta yanke.

Ya bayyana haka ne a wajen bude sabon ofishinsu a Abuja.

Asante ya ce kaso 30 ne kadai na hukuncin da suka yanke aka aiwatar.

Ya ce kotun na taka muhimmiyar rawa wajen abin da ya shafi samar da zaman lafiya da gwamnati ta gari da kuma gudanar da al’amura yadda ya kamata.

Asante, ya kuma tabbatar da cewar za su ci gaba da ba da tasu gudunmuwar da ta kamata ganin yadda kotun ke zama babban tubali ga ECOWAS.

Shi ma Shugaban Hukumar Gudanarwar ta ECOWAS, Dokta Alieu Touray, ya nuna rashin jin dadinsa da yadda kasashe mambobin kungiyar ba sa aiwatar da hukuncin kotun, don haka ya bukaci su yi watsi da waccan dabi’ar.

Ya kuma ba da tabbacin cewa samar da sabon ofishin zai samar wa kotun dukkanin abin da take bukata wajen gudanar da aikinta cikin tsari.