✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya zama sabon Shugaban ECOWAS

Wannan ne karo na farko da Tinubu ya halarci taron ECOWAS tun bayan rantsar da shi a matsayin Shugaban Kasa.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya zama sabon Shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS.

An sanar da shi ne a yayin taron kungiyar na 63 wanda ake yi a Guinea Bissau a yau Lahadi.

Tinubu ya karbi jagorancin kungiyar ne daga hannun Shugaban na Guinea Bissau, Umaro Embalo.

Wannan ne karo na farko da Tinubu ya halarci taron na ECOWAS tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

A makon jiya ne Shugaba Tinubu ya karbi bakuncin Shugaba Embalo a birnin Legas, inda ya ce sun ci abinci tare kuma “mun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafe mu.”

A wancan lokacin, Tinubu ya ce babban burinsa shi ne ya sake mayar da kasar jagora ga sauran kasashen nahiyar Afirka.