✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya tafi Birtaniya ganin likita

Kasa da mako biyu bayan dawowar matarsa daga Dubai inda ta yi kusan wata shida

Jirgin Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi zuwa birnin London na kasar Birtani inda Shugaban Kasar zai ga likita.

Shugaban Kasar ya yi tafiyar ce bayan jagorantar zaman Majalisar Tsaro ta Kasa, inda ya umarci shugabannin tsaro da suka kamo ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da masu daukar nauyinsu.

Buhari ya gargade su cewa hana migayun yin motsi shi ne babban aikinsu fiye da daukar mataki bayan an aikata laifi ba.

Wannan ita ce tafiyarsa kasar waje ta farko a 2021, kuma rabonsa da tafiya kasar waje tun watan Janairun 2020, inda ya halarci Taron Tattalin Arzikin Birtaniya da Afirka.

Tafiyar tasa ta zo ne kada da mako biyu bayan dawowar matarsa, Aisha Buhari daga birnin Dubai, inda ta ga likita, ta kuma shafe kusan wata shida.