✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Buhari ya soke karin kudin mai da lantarki ko ya sha mamaki’

Kungiyar ’yan Arewa ta bukaci a soke karin farashin saboda ya jefa mutane cikin kunci

An yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta soke karin da aka yi farashin man fetur da wutar lantarki domin guje wa zanga-zanga.

Wata kungiya rajin kare muradun Arewa (CNG) ta bukace shi ya mayar farashin mai N145 na wutar lantarki kuma N23 domin kauce wa gangamin kalubalantar karin farashin a fadin Najeriya.

Kakakin kungiyar, Abdulaziz Suleiman ya ce, “Matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka a ’yan kwanakin nan na kara farashin muhimman abubuwa kamar wutar lantarki da man fetur ya fuskanci Allah-wadai daga al’ummar kowanne bangare na Najeriya.

“Bayan damuwa da nuna takaici kan irin wannan matsin da aka jefa ’yan kasa, CNG ta yi taro a Kaduna domin duba halin tsadar rayuwa, halin talauci da kuma matsalar rashin tsaro.

“Taron ya tattauna kan yadda hukumomi suka kasa habaka tattalin arziki, tsaro da kuma hadin kan kasa, wadanda su ne suka zama ummul-aba’isun halin da jama’a su ka tsinci kansu.

“Abin takaici ne matuka cewa duk da irin alkawuran da gwamnati mai ci take yi na yaki da cin hanci da rashawa, kusan za a iya cewa gwamma jiya da yau musamman in aka yi la’akari da matsayin Najeriya a ma’aunin yaki da rashawa na duniya”, inji sanarwar.

Kazalika, kungiyar ta Arewa ta ce an yi wa gwamnati mai ci duk irin uzurin da ya kamata, duk da cewa har yanzu ita ba ta yi abin da ya kamata ba.

Kungiyar ta lissafa abubuwa da dama da farashinsu suka yi tashin gwauron zabo kamar harajin kayayyaki na VAT daga kaso biyar cikin 100 zuwa 7.5, farashin shinkafa, masara, takin zamani, kudaden kasashen waje da sauransu.

A cewar kungiyar kare-karen sun kara taimakawa wajen kara jefa alu’mma cikin halin matsi da takura.

Ta ce abin takaici ne yadda gwamnati ta damka ragamar kayyade farashin mai kacokam a hannun kungiyar dillalai ta IPMAN, wanda hakan ke nuna gazawarta.