✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya sake sabunta wa’adin shugabannin JAMB da NUC da UBEC

Hakan ya biyo bayan shawarar da Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya bayar.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake sabunta wa’adin Farfesa Ishaq Oloyede a matsayin Shugaban Hukumar Samar da Guraben Karatu a Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) da kuma Farfesa Abubakar Adamu Rasheed a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC).

Hakan ya biyo bayan shawarar da Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya bayar.

Dukkan nade-naden guda biyu na tsawon shekara biyar ne masu zuwa, kuma sun fara aiki ne daga ranar daya ga watan Agustan 2021.

Kazalika, Shugaban ya kuma amince da sake nadin Dokta Hamid Bobboyi a matsayin Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimin Bai-daya ta Kasa (UBEC), shi ma a karo na biyu.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Ben Bem Goong ya fitar ranar Juma’a a Abuja.

Dukkan mutum ukun dai wa’adin mulkinsu na farko ya kare ne a hukumomin nasu, tare da karin wasu hukumomin na gwamnati guda 11.

Sanarwar ta kuma ce gabanin haka, shugaban ya kuma amince da nadin Farfesa Ifeoma Isiugo-Abanihe a matsayin shugaban Hukumar Shirya Jarrabawar Kasuwanci da Fasaha ta Kasa (NABTEB) na tsawon shekaru hudu, domin ta ci gaba da wayar da kan jama’a a kan muhimmancin ilimin sana’a da kuma na fasaha.