Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan Kudurin Dokar Man Fetur (PIB) mai cike da cece-kuce.
Shugaban ya sanya hannun ne ranar Litinin, kamar yadda kakakinsa, Femi Adesina ya tabbatar a cikin wata sanarwa.
Ya ce yin hakan na daya daga cikin sauke alhakin da Kundin Tsarin Mulkin kasa ya dora masa.
Kudurin dai na kunshe da sassa guda biyar da suka hada da shugabanci da hukumoni, gudanarwa, raya yankunan da ke da arzikin mai, tsara hanyoyin kashe kudaden mai, da kuma sauran tanade-tanade a cikin sadarori 319 da kuma bangarori guda takwas.
“Za a gudanar da bikin sabuwar dokar a hukumance ranar Laraba, lokacin da kwanakin killace kai na tilas da Shugaban ke yi za su cika,” inji sanarwar.
Tun da farko dai Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da kudurin ya zama doka, duka kuwa da yadda ya jawo cece-kuce matuka da kuma tayar da kura.