A ci gaba da kokarin hada ‘yan Jam’iyyar APC domin su zama tsintsiya madaurinki daya, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya daura nauyin tattaunada da yin sulhu tsakanin ‘yan Jam’iyyar APC a kan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Babban mai taimakawa shugaban kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu a sanar da hakan.
Ayyukan da Tinubu zai yi, sun hada da raba gardama tsakanin ‘yan jam’iyyar da rikicin shugabancin jam’iyyar da kuma masu rike da mukamai a wasu jihohin kasar.