✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya nada sabon shugaban NCDC

Adetifa dai zai maye gurbin Ihekweazu, wanda ya sami sabon matsayi a WHO.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Dokta Ifedayo Morayo Adetifa a matsayin sabon shugaban Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC).

Kakakin Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Litinin.

Adetifa dai zai karbi ragamar shugabancin NCDC ne daga Chikwe Ihekweazu, wanda ya sami sabon matsayin Mataimakin Darakta Janar na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

A cikin wata wasika da aka aike wa Ihekweazu a hukumance, Shugaban WHO, Tedros Ghebreyesus ya ce Najeriya ce ke rike da mukamin mai kula da kai dauki kan cututtuka a hukumar ta lafiya.

Wasikar ta kuma ce zai fara aiki ne ranar daya ga watan Nuwamban 2021 kuma zai rika kula da sashen hukumar mai kula da annoba da ke birnin Berlin na kasar Jamus.

Shugaba Buhari ne dai ya nada Iheakweazu shugabancin NCDC a 2016.

Sabon shugaban na NCDC dai mamba ne a kwamitin farfado da bangaren lafiya da Shugaban Kasa ya kafa ranar Litinin.

Ya kammala karatun digirinsa na farko a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara.

Ya kuma kammala samun horo a bangaren lafiyar yara na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas da ke Idi-Araba, sannan ya yi digirinsa na biyu da na digir-gir a bangaren cututtukan masu yaduwa a Jami’ar birnin Amsterdam da ke kasar Netherlands.